Yusuf Shuaibu" />

Nijeriya Ta Za Bunkasa Tattalin Arzikinta Ta Hanyar Sufurin Ruwa – Gbemisola Saraki

karamin ministar sufuri, Sanata Gbemisola Saraki ta bayyana cewa, tsarin sufurin ruwa zai taimaka wa Nijeriya wajen bunkasa zuba jari na kasashen waje wanda aka samar a bakin iyakokin Nijeriya. Saraki ta bayyana hakan ne a Jihar Legas wajen taron masu ruwa da tsaki a harkokin sururin ruwa wajen samar da daftarin manufofi. Ministar ta bayyana cewa, manufofin zai tallafa wa Nijeriya wajen gudanar da yarjejeniyar kasuwancin kasashen Afirka. An dai fara gudanar da wannan kassuwancin ne tun a shekarr 2018, wanda ya bankasa a duniya, inda aka shirya a ranar 1 ga watan Junairun shekarar 2021.

Taron wanda ma’aikatan sufuri ta shirya domin samun shigar da masu ruwa da tsaki cikin manofofin sufurin jiragen ruwa. Ana tsammanin manufofin sufurin jiragen zai canza tsarin gudanarwa na sufurin ruwa kasar nan ta yadda zai dace da na kasa da kasa, domin samun tattalin arziki mai yawan gaske.
Saraki ta jaddada cewa, sufurin jiragen ruwa yana da matukar mahimmanci wajen bunkasa tattalin arziki. Ta kara da cewa, samar da manufofin sufurin ruwa zai yi matukar farfado da tattalin arzikin Nijeriya. A cikin jawabin ministar da ta gabatar a wajen taro ta bakin sakataren dun-dun-dun na ma’aikatan sufuri, Dakta Magdalene Ajani ta bayyana cewa, wannan manufofi na sufurin jiragen ruwa zai kasancewa ka’idoji ne da ke kulawa da ayyukan sufurin ruwa wanda zai bunkasa bangaren bakin tekun Nijeriya. Ta kara da cewa, wannan kundi ne da zai taimaka wajen fadada kasuwanci a duniya. Ta ci gaba da cewa, wannan kundi ne da zai yi matukar inganta harkokin kasuwancin sufurin ruwa. A cewarta, tsarin manufofin sufurin ruwa na kasa zai taimaka wa kasar nan wajen gyara tattalin arzikinta a dai-dai lokacin da kasar take fuskantar matsin tattalin arziki wanda take neman hanyoyin da za ta fita daga cikin wannan matsala.
Saraki ta ce, “wannan tsarin na sufurin ruwa zai taimaka wa Nijeriya wajen samun alfanun yarjejeniyar harkokin kasuwanci na yankunan Afirka, wanda Nijeriya ta rattaba hannu da kungiyar bunkasa yankunan Afirka. Wannan yarjejeniya zai tallafa wa shugabancin Nijeriya idan aka bi tsarin yadda ya dace. Idan aka bi ka’idojin da aka gindaya ya gudanar da kasuwancin yankunan Afirka, to zai taimakawa yankunan wajen gudanar da saye da sayarwa na kasa da kasa.”
A cikin jawabinsa, sakataren dun-dun-dun ya bayyana cewa, an dauko hanyar gyara bangaren sufurin ruwa wanda za a amfana a nan gaba kadan.
Ajani ya ce, “kamar yadda kowacce kasa take, Nijeriya ta gano mahimmancin da manufofi aiwatar da tsarin sufurin ruwa. Wannan hanyar ce da ke bunkasa bangaren sufurin ruwa cikin dan karamin lokaci tare da samun albanun harkokin kasuwanci da kowacce kasa a duniya.”
Shugaban kwamitin tsarin manufofin sufurin ruwa, Dakta. Paul Adalikwu ya bayyana cewa, babu wani gwamnati da za ta sami nasara ba tare da manufofi ba musamman ma a bangaren da ke da matukar mahimmanci. Adalikwu ya bayyana cewa, wannan kundin manufofi na sufuri zai bunkasa harkokin kasuwanci domin samun kudaden shiga.
Daga cikin mahalatta taron sun hada da shugaban kwamitin majalisa a bangaren sufurin ruwa Sanata Danjuma Goje da wakilan kwamitin majalisar wakilai da Hon. Lynda Ikpeazu. Sauran sun hada da kungiyar masu sufurin ruwa na Nijeriya, Misis Margaret Orakwusi da shugaban masu gudanarwa na sufurin ruwa Otunba Kunle Folarin da shugaban kungiyar masu fito na bakin teku Dakta MkGeorge Onyung. Ita ma shugaban hukumar kula da tashoshin ruwa, (NPA), Hadiza Bala Usman ta halarci taro da shugaban hukumar kula da jefen bakin teku, Dakta George Moghalu. Haka kuma, akwai shugaban gudanarwa na bayar da agajin gaggawa na bakin teke Dakta Bashir Jamoh da wakilin daraktan gudanarwa na kudade, Mista Chudi Ofodile. Sannan kuma akwai wakilai daga kowani bangarorin ma’aikatan sufuri ta tarayya a wajen wannan taro.

Exit mobile version