Nijeriya Tana Bukatar Gudanar Da Zaben Raba Gardama Kafin 2023 – Kungiyar ARP-M

Zaben

Daga Yusuf Shuaibu,

A dai-dai lokacin da zaben shekarar 2023 ke karatuwa, kungiyar ARP-M ta bayyana cewa ya kamata a gudanar da zaben raba gardama na kasa a matsayin hanyar da zai magance matsalolin da Nijeriya take fuskanta a halin yanzu. Kungiyar ta bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ta kira a ranar Asabar.

Bisa halin da kasar nan ke ciki, “ba ma jin dadin abubuwan da suke faru a cikin kasar nan, saboda haka ne ya sa muke kira da a yi kokarin canza al’killar Nijeriya a farkon shekarar 2022 ta hanayar gudanar da zaben raba gardama na kasa domin dakile wasu matsaloli da kasar nan ke fuskanta.”

A cewar kungiyar ARP-M, wasu matsalolin da kasar nan ke fuskanta sun hada da masu neman ballewa da rashin ayyukan yi da rashin tsaron rayuka da na dokiyoyi. Kungiyar ta bayyana cewa lokacin da aka magance wadannan matsaloli za a samu kyakkawan dimokaradiyya a babban zaben shekarar 2023 ba tare da rabuwan kawunan ‘yan Nijeriya ba.

Da yake jawabi ga manema labarai a Jihar Legas, shugaban kungiyar, Ambassador Mutiu Kunle Okunola ya bayyana cewa an samu gazawa a cikin Jamhuriyya na hudu sakamakon amfani da kundin tsarin mulkin da marigayi Sani Abacha lokacin mulkin soja wajen dawo da mulkin dimokaradiyya, domin ya ci gaba da zama a karagar mulki.

Ya ce, “hakazalika gwamnatin jam’iyyar PDP a shekarar 1999 ta gudanar a cikin burinta. Kundin tsarin mulki bai dace da al’umma mai sharkakkakiya kamar Nijeriya da ke da kabilu masu yawa da addinai.

“Duk da haka, sakamakon wannan kundin tsariin mulki da muka gada daga gwamnatocin baya, baya tafiya da tsarin ra’ayin mutane da siyasarmu da tattalin arzikinmu a Nijeriya.

“Gwamnati tana ci gaba da jarorancin kasa cikin cin hanci da rashawa da rashin adanci wanda yake janyo kashe-kashe da ayyukan ‘yan bindiga da neman ballewa da kabilanci da nuna bambancin addini da dai sauran su, wanda Turawan mulkin mallaka suka raba mu tun kafin samun ‘yancin kai.

Exit mobile version