Connect with us

WASANNI

Nijeriya Tana Da Manyan ’Yan Wasa -SIMEONE

Published

on

Mai horar da kungiyar Atletico Madrid Diego Simeone, ya ce tawaga ta 2 ta ‘yan wasan Nijeriya Super Eagles ta kunshi kwararru da za su iya buga wasanni a manyan kungiyoyin kwallon kafa da ke nahiyar turai. Simeone ya bayyana haka ne bayan kammala wasan sada zumunci tsakanin ‘yan wasansa na Atletico Madrid da Nijeriya inda suka samu nasara ta kwallaye 3-2, a filin wasa na Godswill Akpabio, da ke garin Uyo, na jihar Akwa Ibom.

Mai koyarwar na Atletico Madrid ya bayyana wasan da mai horarwa na Super Eagles Salisu Yusuf ya jagoranta da cewa ba wasa ne mai sauki ba, wanda ya kagu a kammala saboda fargabar yin rashin nasara a hannun ‘yan Nijeriyar. ‘Yan wasan Nijeriya Usman Mohammed da Kelechi Nwakali ne suka ci wa Super Eagles kwallayenta 2, yayin da Angel Correa, Fernando Torres da Borja Garces suka ci wa Atletico Madrid kwallaye 3. A makon da ya gabata ne Atletico Madrid ta lashe kofin gasar Europa, bayan lallasa Marseille da ci 3-0.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: