Nijeriya Tana Daga Cikin Kasashe 22 Masu Fama Da Tarin Fuka Farfesa Etete Peters

Daga Idris Aliyu Daudawa

Wani sabon rahoto wanda kungiyar da ake kira NigeriaThoracic Soceity  ta fitar, ya kuma nuna cewar Nijeriya tana daga cikin kasashen 22, wadanda suke fama da tsananin bala’in cutar tarinfuka, a duniya, wanda kuma shi en babbar matsala a Afirka.

Kididdigar ta nuna cewar kashi uku na yawan al’ummar duniya suna fama da cutar Mycobacterium tuberculosis, bayan haka kuma da akwai sabuwar cuta ko wace dadika.

Wadannan bayanan an bayyanasu ne jiya a Uyo, wanda shugaban kungiyar Nigeria Thoracic Soceity Farfesa Etete Peters, a ranar da ake bikin ranar tarin fuka ta duniya, ta wannan shekara wadda take da taken ‘’Bukatar shugabannin zasu jagorancin fafutukara duniya ta kasance ba tarin fuka’’.

Ya kara bayyana cewar tarin fuka shi ne cutar da take jagoranci daga cikin masu kisa, saboda ku san mutane fiye da milyan daya da dubu dari bakwai,ne suke mutuwa ko wace shekara, wannan shi ne abu na tara da ke zama sanadiyar mutuwar mutane a duniya.

‘’Wannan rana wani bikine domin a samu yadda za ahada kai a siyasance da kuma zamantakewa,domn a samu hanyar da za a kawo karshen ita cutar tarin fuka, a matsayin wadda ta addabi mutane’’.

Taken ranar bikin tarin fuka ta duniya ta wannan shekara ita ce ‘’ Bukatar shugabanni su bada hadin kai wajen yakar cutar tarin fuka, ya kasance an gama da ita gaba daya’’.Ya ce mayar da hankalin da za a yi wajen an hada karfi da karfe domin kawo karshen tarin fuka, ba wai sai da shugabannin siyasa kadai ba, wto shugabannin kasashe, da kuma Ministoci ma’ikatun lafiya, amma kowa ya kamata ya bada tashi gudunmawa, shugabannin Kananan Hukumomi, gwamnoni, ’yanmjalisu, shugabannin al’umma, da mutane wadanda suke dauke da cutar tarin fuka, kungiyoyi masu zaman kansu, ma’aikatan lafiya, Liktoci, ma’aikatan jiyya, Kungiyoyi masu zamankansu,da kuma sauran masu taimakawa, da kuma shugabanni masu taimakawa kokarin da ake dangane da shirin da ake na kawo karshen cutar tarin fuka.Farfesa Peters shi ne tsohon shugaban asibitin koyarwa na jami’ar Uyo ya bayyana cewar  tarin fuka, yana shafar shekarun ma’aikata wadanda suke taimakawa wajen ci gaban tattalin arziki . Wata babbar matsala ita ce duk cikin mutum uku,daya yana dauke da cutar fuka, ba  a taba duba shi ba, bayan hka kuma a Nijeriya anaiya samunkashi 50 cikin dari,wannan ya nuna ke nan ba za ayi masu magani ba, sune kuma zasu rika yada cutar a wuraren da suke.

Farfesa Peters ya ce abin da aka mai da hankal a wannan shekara, yana da nasaba da, muradun ci gaba, domin a yaki cutar tarin fuka. Sai kuma tsarin duniya na a kawo karshen cutar tarin fuka tsakanin shekara 2016 da kuma 2020, wannan duk ana harin shekarar 2031 wadda ake fatar kawo karshen cutar tarin fuka gaba daya.

Exit mobile version