Abba Ibrahim Wada" />

Nijeriya Za Ta Buga Wasa A Legas Karon Farko Bayan Shekara 20

Jihar Legas za ta karbi bakuncin wasan tawagar kwallon kafa ta Najeriya a karon farko tun bayan shekara 20 kamar yadda hukumar kula da wasannin kwallon kafa ta kasa ta bayyana wa manema labarai a ranar Litinin..

Super Eagles za ta kara da tawagar ‘yan wasan kasar Lesotho ranar 30 ga watan Maris a wasan neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za su yi a filin wasa na Teslim Balogun dake jihar ta Legas.
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF ta ce yawan mutanen da za su kalli karawar ya ta’allaka kan matakan hana yada cutar korona da hukumar kwallon kafa ta Afirka, CAF da za fitar kafin lokacin fafata wasan.
Wasa na karshe da Super Eagles ta buga a Legas shi ne a watan Janairun shekara ta 2001 wanda ta doke kasar Zambia a fafatawar shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka kuma tun daga wancan lokacin ba’a sake kai wasan Nigeriya jihar Legas ba.
Sai dai a shekarar 2011, Najeriya ta buga wasan sada zumunta da tawagar kasar Saliyo, inda ta yi nasara a filin wasa na Teslim Balogun a jihar ta Legas da ci 1-0 wasan daya dauki ‘yan kallo masu yawa.
Ministan wasanni na Najeriya, Sunday Dare ya ce filin wasa na Legas zai ci gaba da karbar bakuncin wasannin kasar da zarar an kammala gyaran katafaren filin saboda haka nan gaba za’a dinga yawan kai wasa jihar.
Super Eagles ta ci gaba da yin wasanninta a wasu jihhohin fadin kasar, bayan da hukumar kwallon kafar Najeriya wato NFF kan tuntubi wadda keda sha’awar karbar bakuncin wasannin na kasa.
Duk jihar da ta karbi bakuncin Super Eagles kan taimaka da kudi wajen gudanar da wasannin kamar yadda ta buga a birnin Port Harcourt da Kano da Cross Riber da Akwa Ibom da Delta da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Exit mobile version