Connect with us

Uncategorized

Nijeriya Za Ta Buga Wasa Da Libiya A Kaduna

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles za ta karbi bakuncin kasar Libya a wasan fafutukar fitowa zuwa kofin nahiyar Afrika a filin wasa na Ahmadu Bello dake Kaduna kamar yadda hukumar kwallon kafar kasa nan ta bayyana.

Shugaban sashin yada labarai na kungiyar ta Nijeriya Toyin Ibitoye ne ya shaidawa manema labarai hakan a shafinsa na Twitter a safiyar ranar Litinin.

Da farko dai wasan za a buga shi ne a ranar 10  ga watan Oktoba da misalin karfe 5:30pm na yamma amma yanzu hukumar kwallon kafar Afirka, CAF ta amince a mayar da wasan ranar Juma’a 12 ga wata.

Suma Libyan zasu karbi bakuncin Nijeriyar a ranar 15 ga watan Oktobar a kasar Tunisia mai makon kasar Algeria da tun farko a nan aka tsara za a buga wasan na biyu.

Alkalin wasa Jean Jackues Ndala Ngambo dan kasar Congo shine zaiyi alkalanci a wasan sannan kuma Olibier Safari, wanda shima dan kasar Congo ne shine zai taimaka masa tare da taimakon mahutan alkalan wasa Kebene da Nabina Balise Sebutu.

Nijeriya dai sune na uku a rukunin E da maki 3 bayan ta buga wasanni biyu yayinda Libya take matsayi na daya da maki hudu sai kuma kasar Afirka ta kudu a matsayi na biyu itama da maki uku.

Advertisement

labarai