Daga ranar 1 ga Oktoba, 2025, hukumar kula da shige da fice ta Nijeriya (NIS) za ta fara ɗaukar mataki a duk faɗin ƙasar kan ‘yan ƙasashen ƙetare da suka tsallake kwanakin bizarsu ko kuma suka saɓa ka’idojin shigowa ƙasar.
Dokar za ta fara aiki akan waɗannan rukunin ‘yan ƙasashen wajen da suka haɗa da:
Masu riƙe da bizar zuwa ziyara (VoA), bizar kasuwanci da kuma bizar ‘yancin zama (CERPAC).
‘Yan ƙasashen ƙetare da suka karya dokar shige da fice ta Nijeriya za su fuskanci hukunci, wanda zai iya haɗawa da tara, kora, ko kuma yiwuwar hana sake shigowa Nijeriya nan gaba.