Connect with us

KASUWANCI

Nijeriya Za Ta Fara Wanzar Da Aikin Tsarin Tattara Bayani Don Tallafawa Tattalin Arzikin Basa

Published

on

Gwamnatin tarayya a shirye take don fara wanzar da aikin rijistar tsarin tattara bayanai a basar, inda za ta fara baddamar da fara aikin a birnin tarayyar Abuja.
Shugaban aiwatar da shirin Dakta Anthony Uwa ne ya sanar da hakan a hirar sa da kafar dillancin labarai na basa a Abuja, inda ya bara da cewar, gwamnatin tare da hadin gwaiwa da shirin BRISIN da kamfanin Dermo Imped da wadanda tuni suka fara gudanar da gangamin wayar da kai akan aikin.
Shirin na BRISIN zai tattara bayanai ne da tara su da kuma rarrabar da bayanai don taimakawa kula da tattalin arzikin Nijeriya.
Tuni dai gwamnatin tarayya ta amince da wanzar da aikin wanda kamfanin Dermo Imped dake basar Italiyan zai yi kwangilar aikin.
Anthony Uwa ya ci gaba da cewa, zagayen aikin na biyu shine baddamar da aikin a hukumance, inda a nan ne za a fara gudanar da aikin gadan-gadan.
A cewar sa, don a cimma nasarar aikin ne ya sanya aka tanadin dukkan kayan aikin da ake bubata kafin baddamar da aikin da kuma ganawar da aka yi da masu ruwa da tsaki.
Ya bara da cewa, mahukuntan birnin tarayyar Abuja ne su samar da kudi da samar da ofishin wanzar da aikin don baddar da aikin kafin kamfanin BRISIN ya giggina cibiyoyi.
A cewar sa, gwamnatin tarayya ta umarce mu damu nemi kudi daga gun ‘yan basa da kuma bungiyoyin dake basashen waje.
Uwa ya bayyana cewar, tawagar aiwatar da aikin za su nemi kudi don fara gudanar da aikin ta hanyar yin amfani da ‘yan balilan masu zuba jari wadanda tuni suka fara tallafawa aikin.
Shugaban ya bayyana cewar, shirin na BRISIN zai kai tsawon shekaru sama da goma zuwa sha biyar da za a gudanar dashi a daukacin fadin Nijeriya.
Har ila yau, Uwa yace nan bada jimawa ba za a baddamar shirin na BRISIN a Abuja a barshen wannan shekarar, da tuni mun kammala sanya kayan aikin da yin gini inda akwai wadatattun kudi.
A cewar Uwa,“mun gana har sau biyu, kuma muna aiki ne da hukumomin yawan alummar bas(NPC) da hukumar tattara haraji ta basa ta tarayya (FIR) da kuma humukar bididdiga ta basa(NBS).”
A cewar sa, dukkan abubuwan da ake bubata akan mutane da bayanan su da yankunan da suke da zama da kuma lambar tsaro, wannan shine dalilin da yasa muke bubatar yin aiki da wadannan manyan hukumin uku don wanzar da aikin da kuma nubatar bayanan banki.
Uwa ya yi nuni da cewar, “Ina son in baku tabbacin cewar, da zarar mun fara baza mu tsaya ba, kuma aikin na Abuja zai kai watanni shida ana gudanar dashi, in har an samar da wadatattun kudi.
Shugaban ya bayyana cewar, ganawar da aka yi guda biyu a watan Mayu da masu ruwa da tsaki, anyi ne don yadda za a tinkari aiwatar da aikin kamar yadda gwamnatin tarayya ta yarda.
Ya bayyana cewar, gwamnatin tarayya tace mahukuntan birnin tarayya, su samar kayan aiki musamman ofishi don baddamar da shirin na BRISIN, inda za a fara da tattara bayanai, inda daga nan, za ta samar da fili don shirin na BRISIN wajen samar da cibiyoyi tun daga mazabu har zuwa jahohi.
Uwa ya ci gaba da cewa, ganawar ta biyu da aka gudanar ya haifar da sakamako mai kyau, inda ganawar ta nuna, lokaci ya yi da za a samar da ci gaba.
Kamfanin dillancin labarai na basa ya ruwaito cewar, kimanin ma’adanar tattara bayani gudan 9,822 za a kafa tun daga mazabu zuwa jahohi a basar nan don gudanar da aikin, inda ko wanni ma’adanar tara banain guda daya za ta sanya guda 8,812 a mazabu a Nijeriya sannan kuma a gusa zuwa bananan hukumomi 774 da ake dasu a basar nan.
Shirin na BRISIN, tsohuwar gwamnatin shugaban basa Cif Olusegun Obasanjo ce ta birbiro dashi, inda kuma tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan ta baddamar da kwamitin wanzar da aikin.
Advertisement

labarai