Yusuf Shuaibu">

Nijeriya Za Ta Samu Rarar Sama Da Naira Tiriliyan Bayan Cire Tallafin Mai–Sylva

karamin ministan albarkatun mai, Timipre Sylva, ya bayyana cewa, Nijeriya za ta samu rarar sama da naira tiriliyan daya a duk shekara, sakamakon cire tallafin mai.
Ministan ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja. Ya bayyana cewa, an samu nasarar tanadar naira biliyan 500 daga wadannan kudade wajen aiwatar da kasafin kudin shekarar 2020. Ministan ya kara da cewa, bisa yadda aka gyara bangaren mai, zai saukaka wa masu zuba jari wajen samun daman zuba jari a matatun mai da ke kasar nan. Ministan ya ce, cire tallafin mai ba karamin alkairi ba ne ga ‘yan Nijeriya.
“Sakamakon cire tallafin mai ya sa Nijeriya ta samu nasarar tattalin biliyoyin kudade a duk shekara. A cikin kudaden da ake bayar da tallafin mai aka samu nasarar tanadar naira biliyan 500 daga cikin kasafin kudin 2020.
“Idan muka duba za mu ga cewa, a lokacin da ake bayar da tallafin mai mutane tsiraru ne suka amfana da wannan kudade. Kuma wadanda suke amfana masu kudi ne ba wai talakawa ba, amma a halin yanzu talakawa ne ke amfana da rarar kudaden cire tallafi.
“Tsarin cire tallafin mai alkairi ne ga talakawar Nijeriya, domin zai bayar da damar samun alfanu masu yawan gaske.
“Idan da a ce muna iya tace mai a Nijeriya, to ana tsammanin sayar da mai da bayar da tallafi. Ta yaya za a samu nasarar samun damar tace mai bayan babu mai son zuba jari a bangaren matatun mai na Nijeriya.
“Idan aka zuba jari mai yawa a wannan bangare, to za a samu damar makin ayyukan yi a Nijeriya. Sannan gyara fannin ya sa ‘yan kasuwan za su iya shigo da mai da kansu kuma su sayar da shi a Nijeriya. Wannan ya sa an samu matukar ayyukan yi ga mutane. Bisa yadda aka gyara fanni, an samu ayyukan yi da dama a Nijeriya.
“Sakamakon gyara fannin ya sa an samu alfanu mai yawan gaske, sannan muna tsammanin samun zuba jari a Nijeriya wajen gina matatun mai ta yadda za a dunga tace man a nan cikin gida Nijeriya tare da an fitar da shi kasashen ketare ba. Hakan ya saukaka wa kamfanin mai na kasa wajen tsara samun kudaden gyara matatun man da Nijeriya ke da su,” in ji shi.

Exit mobile version