Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa, tabbas Nijeriya za ta yi hannun riga da shiga cikin matsin tattalin arziki. Wanda a karon farko Nijeriya ta shiga cikin matsin tattalin arziki wanda ba ta taba fuskantan hakan ba tun bayan shekaru 33 a wannan shekara. Duk da fuskantar matsalar hauhawar farashin kayayyaki da ake samu a Nijeriya, kwamitin harkokin kudaden ya kawo manufofin da aka samu nasarar rage na kashi 11.5, inda manufofin za su ci gaba da aiki wajen farfado da tattalin arzikin kasar nan, yayin da CBN yanke kokarin samun tallafin wasu bangarorin tattalin arziki domin kawo dauki wajen fita daga cikin matsin tattalin arzikin. Kwamitin ya jaddada cewa, za a samu bunkasa tattalin arziki a dan karamin lokaci da jimawa ba.
Gwamnan CBN, Mista Godwin Emefiele ya bayyana cewa, akwai bayanai daga bangaren mahimman fannukan tattalin arziki da suka bayar da shawarwari wajen farfadowa daga cikin matsin tattalin arziki kafin kasarshen shekarar 2020, sakamakon ayyukan tattalin arzikin da suke gudanarwa a bayan fage a halin yanzu. A cwarsa, ana tsammanin tattalin arzikin zai farfado kafin kasarshen shekarar 2020, yayin da za a magance hauhawar farashin kayayyaki kashin farkon shekarar 2021 wanda hakan zai kyaura lamurar da suka lalace a cikin fannonin tattalin arziki a wannan lokaci.
Mambobi guda 10 ne kacal daga cikin ‘yan kwamitin suka halarci taron kwamitin na baya a cikin shekarar 2020, haka kuma ana fatan kwamitin ya ci gaba da gudanar da wasu tsare-tsare da za su bayar da goyar baya wajen bunkasan tattalin arziki tare da kayyade rage ayyukan yi da bayar da dama ga ‘yan kasuwa masu zuba jari da kuma bayar da goyan bayan da ya dace ga bangaren lafiya, domin dakile matsalolin cutar Korona.
“Bugu da karin, CBN tana tsammanin daukan matakai da dama wajen bunkasa harkokin masu hudda da bankuna domin bayar da damar farfadowa daga matsan tattalin arziki.”
Kwamitin ya bayyana cewa, ya samu nasarar rage kudaden ruwa na bayar da bashi wanda haka ya sa aka samu masu amsar basuka domin zuba jarin da zai farfado da tattalin arziki nan take. A watan Oktobar shekarar 2020, an samu tallafin na basuka wanda ya kai na kashi 86.23 ga mutane guda miliyan daya da ke gudanar da harkokin kasuwanci. An samu bunkasar kashi 76.43 a watan Yulin shekarar 2019.
Kwamitin ya kara da cewa, kara bunkasa harkokin kudade ya taimaka wanda aka samu na kashi 15.5 na zabar kudin da ake gudanar da harkokin kasuwanci da na bashi wanda aka samu kashi 5.73 da kuma kudaden da aka samu riba wanda suka kai na kashi 35.6 a cikin watan Oktobar shekarar 2020. Ya ci gaba da bayyana cewa, ana samun wannan nasarar ne sakamakon matakai da CBN tare da hadin gwiwar wannan kwamitin suka dauka na farfado da tattalin arziki a cikin kasar nan, kwamitin ya bukaci bankuna da su yi kokarin cike gurbin da aka samu wajen hada-hadan kudade a cikin kasuwan cinji da sauran hanyoyi da suke samun kudaden shiga. Kwamitin ya kara jaddada cewa, za su ci gaba da bayar da hankalin su ga hada-hadar kasuwancin kasashen ketare,kamar yadda suka gudanar hkarkokin kasuwanci a ranar 19 ga watan Nuwambar shekarar 2020 wanda aka sami ba dala biliyan 35.18, idan aka kwatanta da na watan Satumbar shekarar 2020 wanda aka samu dala biliyan 35.95, a dai-dai lokacin da ake kara samun karuwar farashin danyan mai a kasuwar duniya.
A yanzu haka dai, ana samun matsin tattalin arziki a Nijeriya sakamakon hauhawar farashin kayayyaki. Tarihi ya nuna cewa, ba a taba fuskantar irin wannan tsadar rayuwa ba a Nijeriya kamar yadda ake fuskanta a halin yanzu.