Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ta Nijeriya ‘National Association of Nigerian Traders’ (NANTs), Mr Ken Ukaoha, ya shaida cewar kasar Nijeriya za ta yi asarar sama da naira biliyan dari da arba’in N140b a bisa dage babban zaben kasar.
Ukaoha wanda ya shaida hakan wa (NAN) a Abuja jiya, ya shaida cewar dage zaben ya shafi harkokin kasuwanci kai tsaye.
Ya shaida cewar mafiya yawan ‘yan kasuwa ba su bude shagunansu ba a sakamakon zaton gudanar da babban zaben a jiya.
“Mun kammala shirye-shiryen gudanar da zaben 2019, tun da mun kammala shirin hakan,” Inji shi
Mista Ukaoha ya shaida cewar dagewar zai shafi tattalin arziki ta fuskacin kara yawan fitar da kudade daga gwamnati, jam’iyyun siyasa, da kuma ‘yan Nijeriya a daidaiku a sakamakon wannan lamarin.
Daga bisano Ukaoha ya shawarci ‘yan kasuwa da manoma da su fito su yi zabe a ranar Asabar mai zuwa domin ci gaban kasar nan.
Shugaban hukumar zabe Prof. Mahmood Yakubu, da misalin karfe 2:45 na safiyar jiya Asabar ne ya sanar da dage zaben kasa da awanni da fara gudanar da zaben a kasar nan, inda ya cilla zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya zuwa ranar 23 ga Fabrairu, kana na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi kuma zuwa ranar 9 ga watan Maris a bisa dalilin su na gaza isar da kayayyakin gudanar da zaben a wasu sassan kasar.