Khalid Idris Doya" />

Ninkaya Cikin Tarihi: Masarautar Ningi A Yau

A kwanakin baya ne Sarkin Ningi Alhaji Yunusa Muhammadu Danyaya OON ya cika shekaru 40 a bisa ragamar Sarautar wannan masarauta mai dimbinn tarihi, a bisa haka ne wannan jarida ta yi ninkaya cikin tarihi domin lalobo asalin tarihin Masarautar Ningi da ke karamar hukumar Ningi a cikin jihar Bauchi.

Shi dai Sarki Ningi Danyaya shine Sarki na 15 a cikin jerin saraukunan da aka yi a Ningi tun bayan kafa wannan masarautar wanda Sheikh Hamza ya yi a shekara ta 1827, kuma shine sarkin da ya fi jimawa a karagar mulki.

Masarautar Ningi mai shekaru 191 a yau, tana da dimbinn tarihi na fada a ji wanda kuma tarihinta ya sha banban da sauranta masarautun da suke jihar Bauchi, domin kuwa tarihinta a samo asali ne daga jajircewar da wasu zakakuran bayanin Allah suka yi.

Da fari dai; ita Masarautar Ningi, tana daya daga cikin manyan-manyan masarautun da ke karkashin daular Yakubun-Bauchi; wanda kuma ta hada da masarautu masu tarin daraja.

Wannan Masarauta ta Ningi, kasaitacciyar Masarauta ce da ta kunshi kananan hukumomin Ningi da Warji, wadda akasarin mazaunanta sun kunshi kabilun Fa’awa ne da Warjawa, da Duwa, da Ningawa da kuma Fulani, Masarautar Ningi, tana da yawan al’ummar da kididdiga ta ya nuna cewa sun kai sama da mutum 501,012, wadanda suke zaune a fadin kasa mai girman murabba’in (kilomita) 5,250.

Tarihi ya tabbatar da cewa tun a karni na 18 ne garin Ningi, mazaunin wannan Masarauta ya samo tushen kafuwa, lokacin da wasu shahararrun malaman addinin musulunci su 40, da ke karkashin jagorancin wani mashahurin  malamin Islama Sheikh Hamza suka yo balaguro a cikin shekarar 1827, daga yankin Tsakuwar Kano da ke cikin karamar hukumar Dawakin Kudu ta yau, bayan da suka bijire wa tsarin biyan harajin (kudin kasa) da Masarautar Kano ta lokacin karkashin Sarkin Kano Muhammadu Bello ta bullo da shi. Sheikh Hamza da jama’arsa sun yada zango a yankin Mara da ke cikin Gundumar Toro.

A lokacin da suke a garin na Mara, Shehin malami Hamza, ya ci gaba da aikin da’awar yakar tsarin biyan kudin jiziya da kabilar Fulani masu mulki a lokacin suka tilasta wa mazauna yankin biya, a zamanin mulkin Sarki Dandaura. A shekarar 1830,      Sheikh Hamza ya zamo jagoran al’ummar wannan yanki bayan da ya karya mulkin Sarki Dandaura, daga nan kuma sai ya dukufa ga fadadakarfin ikonsa zuwa ga sauran makwaftan yankunan al’ummomin Butawa da Fa’awa da Warjawa da Kudawa da kuma Sirawa. Sheikh Hamza, ya samu nasarar girka mulki mai tasiri da karfin gaske wanda ya jefa tsoro da shakku a zukatan manyan masarautun Bauchi da Kano da Zariya, masu makwaftaka da shi, wadanda ke yi wa yunkurin kara  fadada karfin ikonsa a matsayin babbar barazana ga masarautunsu. A kan haka ne suka hada karfi da karfe domin ganin bayansa da ganin bayan mulkinsa.

Bayan mutuwar Sheikh Hamza, sai Sarki Ahmadu ya dare halifarsa a shekarar 1850, inda ya yi na tsawon shekara biyar kafin Allah Ya karbi ransa a shekarar 1855, inda, daga nan sai aka zabi Abubakar Danmaje, wanda suruki ne ga marigayi Sarki Hamza. Sarki Danmaje, ya dora ci gaba da aiwatar da dukkan wani abin da ya gada wanda Sarki Hamza ya fara yi, kamar gwagwarmayar fadadakarfin mulkinsa, ya kaddamar da hare-hare har zuwa cikin yankunan masarautun Kano da Hadeja da Katagum da Jama’are da Gombe da Zariya da Birnin Gwari da Kontagora da kuma Wukari, wannan ya ba shi damar kafa wata kakkarfar rundunar dakarun yaki wadda aka fi sani da “Maitabaryar Mashi”. Mulkin Sarki Danmaje ne har-ila-yau ya haddasa sauyin matsugunin jama’ar yankin zuwa tsohon garin Ningi, wanda duwatsu suka yi wa kawanya, daga yanayi da fasalin wannan sabon wurin ne garin Ningi ya samo asalin sunansa. Kalmar Ningi a yaren Butawa na nufin maboya.

Da wannan dama ta kariyar da duwatsu suka yi wa garin Ningi ne, Sarki Danmaje ya zafafa hare-haren fadada karfin ikonsa, har ta kai ga Masarautar Bauchi ta shiga fargabar kutsen Sarki Danmaje, wannan ne ma ya sa Sarkin Bauchi na wancan lokacin ya kafa sabon garin Kafin Madaki, wadda aka kafa ta da manufar taka wa kutsen Sarki Danmaje birki, ta hanyar hanzarta labartawa Masarautar ta Bauchi duk wani yunkurin da Sarki Danmaje zai yi na dannawa gaba zuwa Bauchi.

A cikin shekarar 1870 ne, Allah Yayi wa Sarki Abubakar Danmaje rasuwa, inda Sarki Karami ya maye gurbinsa, wanda shi ma ya ci gaba da yunkurin fadada Masarautar Ningi. A wannan yunkurin, Sarkin Haruna ya samu taimakawar babban mataimakinsa Usman Danyaya, wanda a lokacin yake rike da  Sarautar Barden Ningi. Shi ma dai Sarkin Ningi Haruna, shekaru 16 ya yi yana mulki, inda ya rasu a shekarar 1886. Daga nan sai aka zabi Abubakar Gajigi a matsayin sabon Sarki, wanda shi kuma ya yi tsayin daka wajen wajen ganin Masarautar Ningi ta ci gaba da tsayuwa da kafafunta ba tare da hasarar ko da taku daya na kasarta ba ga wata masarauta.

Bayan rasuwar Sarkin Ningi Abubakar Gajigi ne, sai Sarki Usman Danyaya, wanda shi ne Barden Ningi a zamanin mulkin Sarkin Ningi Haruna, ya zama sarkin Ningi, wanda a zamaninsa ne Turawan mulkin mallaka suka zabi Ningi a cikin zababbun garuruwan da aka kafa hukumomin N.A a duk fadin yankin Arewacin Nijeriya, a daidai shekarar farko ta shigowarsu kasar.

Sarki Mamuda, shi ne ya gaji Sarki Usman Danyaya, daga nan kuma sai Sarki Musa Dangwido, wanda duka-duka shekara daya yayi a kan mulki, daga shekarar 1905 zuwa 1906, sai aka sake mayar da da Sarki Mallam Mamuda, shi kuma ya yi shekara biyu ne a kan mulki, daga shekarar 1906 zuwa 1908. Daga nan sai Sarkin Ningi Adamu Danyaya, wanda idan aka cire Sarkin Ningi na yanzu wato Alh. (Dk.) Yunusa Muhammadu Danyaya OON, babu wanda ya kai shi yawan shekaru a kan mulkin Ningi, domin shekaru sama da 40 cur ya shafe a kan karagar mulkin Ningi.

Masarautar Ningi ta yi Sarakuna a jere har guda 15 tun kafuwarta zuwa yau, wadanda suka hada da: Sarkin Ningi Hamza, wanda ya mulki kasar Ningi (Daga shekarar 1827 zuwa 1850), sai Sarkin Ningi Ahmadu, (Daga shekarar 1850 zuwa 1855), sai Sarkin Ningi Abubakar Danmaje, (Daga shekarar 1855 zuwa 1870), sai Sarkin Ningi Haruna Karami, (Daga shekarar 1870 zuwa 1886), sai Sarkin Ningi Abubakar Gajigi, (Daga shekarar 1886 zuwa 1890), sai Sarkin Ningi Usman Danyaya, (Daga shekarar 1890 zuwa 1890), sai Sarkin Ningi Mamuda Lolo, (Daga shekarar 1902 zuwa 1905), sai Sarkin Ningi Musa Dangwido, (Daga shekarar 1905 zuwa 1906), sai kuma dawowar Sarkin Ningi Mamuda Lolo a karo na biyu a kan karagar mulki, (Daga 1906 zuwa 1908), sai Sarkin Ningi Abdu Mai Fatima, (Daga shekarar 1908 zuwa 1915),  sai Sarkin Ningi Zakari Dankaka, (Daga shekarar 1922 zuwa 1955), sai Sarkin Ningi Adamu Danyaya, sai Sarkin Ningi Haruna Na II, (Daga shekarar 1955 zuwa 1957), sai Sarkin Ningi Abdullahi Adamu, (Daga shekarar 1957 zuwa 1961), sai Sarkin Ningi Ibrahim Gurama, (Daga shekarar 1963 zuwa 1977), daga nan kuma sai Sarkin Ningi mai ci yanzu, wato Alh. Yunusa Muhammadu Danyaya wanda ya dare kan karagar mulkin Ningi a shekarar 1978 har zuwa yau kuma shi ne yake mulkin kasar Ningi.

Mai Martaba Sarkin Ningi Alh. Yunusa Muhammadu Danyaya OON, tarihin Masarautar Ningi, ya nuna cewa shi ne Sarkin da yafi dadewa a kan karagar mulkin kasar Ningi, wanda Allah Ya yi shi Sarkin Ningi tun a shekarar 1978, yanzu kenan yana da shekaru 40 cur a kan mulkin wannan kasaitacciyar Masarauta mai dimbin tasiri da tarihi. Yana daya daga cikin iyayen al’umma da suke da kima da mutunci, ba wai a jihar Bauchi da kadai, har ma ilahirin manyan Masarautun yankin Arewa Maso Gabas da yankin Arewa da ma fadin kasar Nijeriya baki daya.

Adalcinsa da kwatanta gaskiya a tsakanin jama’arsa, ba tare da nuna wata bambanci ba ko kuma wariya a tsakanin al’ummar Masarautarsa, sune sirrin samun nasarar girmamawa da ya ke samu daga jama’arsa, wadana suka dauke shi a matsayin shugaba nagari, jagora kuma Uba a gare su.

Shi dai Sarkin Ningi Alh. Yunusa Muhammadu Danyaya, an haife shi ne a garin Ningi a shekarar 1936, ya soma karatun addini a shekarun farko na kuruciyarsa kafin ya shiga makarantar Elamantare ta garin Ningi, inda ya fara karatun zamani wato karatun boko a shekarar 1941 zuwa 1946. Daga nan, sai ya zarce makarantar Midil ta Bauchi a shekarar 1946, ya yi karatu a makarantar kula da ayyukan lafiya ta Kano a shekarar 1952, kafin daga bisani ya samu zuwa Jami’ar  Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya yi kwas na shekara daya a kan sha’anin mulki daga shekarar 1956 zuwa 1957. Haka kuma ya halarci wani kwas a makarantar British Councilda ke Kano, a tsakanin shekarar 1959 zuwa 1960, sa’annan ya koma Jami’ar Ahmadu Bello a tsakanin shekarar 1960 zuwa 1962, inda ya samu takardar shaidar Difloma a fannin sha’anin mulki.

Ya soma aiki da hukumar N.A a matsayin jami’in kiwon lafiya a asibitin Nasaru da ke cikin karamar hukumar Ningi, a tsakanin shekarar 1953 zuwa 1958. Haka ma ya taba zama mamba a majalisar N.A ta Ningi, tsakanin shekarun 1959 zuwa 1969. Ya rike mukamin Kansila mai kula da harkokin ‘yan sanda da na ma’aikatan gidan Yari.

A shekarar 1959 aka nada Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya a matsayin Uban kasa kuma Ciroman Ningi, ya taba aikin wucin gadi a kamfanin Taba na kasa, a matsayin jami’in kula da jin daddn jama’a, daga bisani sai ya koma hukuma kula da lamurran kasuwanci, daga nan aka kara masa girma zuwa mataimakin manaja mai kula da yankunan Gusau da Kauran-Namoda a shekarar 1968.

A shekarar 1969, an kara daga matsayinsa zuwa manajan Rumbun Ajiye Gyada na yankin Maiduguri, daga nan kuma sai sai likkafarsa ta yi gaba inda aka yi masa manajan shiyya mai kula da yankunan Gombe da Biu da kuma Kano a shekarar 1970. A shekarar 1974 kuwa, an yi masa sauyin wajen aiki yankunan Yola, Mubi, da Mambila. Sannan aka nada shi manajan riko mai kula da yankin Arewa-Maso Gabas a shekarar 1976. Haka ma ya taba zama shugaban kwamitin rarraba kkadarori tsakanin jihohin Arewa da hukumar kula da kasuwanci ta Benuwai da Filato.

A shekarar 1978 ne aka nada Alh. Yunusa Muhammadu Danyaya matsayin Sarkin Ningi, sannan aka kara daga darajarsa zuwa matsayin Emiya mai daraja ta daya a shekarar 1998. Sarkin wanda babban jigo ne a kungiyar Jama’atul Nasril Islam, ya taba jagorancin kwamitin zakka da na kudade na kungiyar Sarakuna ta jihar Bauchi a majalisar Sarakuna ta kasa, daga 1979 zuwa 1983. Haka ma ya taba zama shugaban riko na hukumar Daraktocin Bankin Inland, daga shekarar 1988 zuwa 1991, sannan ya taba zama Daraktan kula da kogunan Hadeja da Jama’are, a shekarun 1989 zuwa 1991.

Mai Martaba Sarkin Ningi, ya taba zama mamba a taron sake fasalin kundin tsarin mulkin kasa, daga shekarar 1994 zuwa 1995. Sannan mamba ne a karamin kwamitin Sarakunan gargajiya a shirin nan na ciyar da kasa gaba na Bision 2010, a tsakanin shekarar 1996 zuwa 1997, ya kuma zama shugaban hukumar Daraktocin makarantar koyon aikin Shari’a da ilimin addinin musulunci ta Misau da ke jihar Bauchi, har na tsawon shekaru uku wato daga shekarar 1996 zuwa 1999.

Ko ba ya ga wadannan ayyuka, mai Martaba Sarkin Ningi Alh. Yunusa Muhammad Danyaya, ya taba zama mamba a kwamitin aikin Hajji na kasa, sannan kuma ya yi

Amirul Hajji na Alhazan jihar Bauchi. Ya taba zama shugaban hukumar yin rajistar jami’an kula da muhalli ta kasa a shekarar 2004, sannan ya taba zama shugaban kwamitin hadin kan addinai na jihar Bauchi a shekarar 2005.

Mai Martaba Sarkin Ningi Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya, ya sha samun lambobin yabo da na karramawa, sakamakon yadda yake ba da gudumawa wajen ci gaban rayuwar al’umma, wannan nema ya sa gwamnatin tarayya ta ba shi lambar girmamawa takasa ta (OON).

Sarki mai ci a yau, duk da shekarun nasa sun dan ja, kasantuwar yau yana da shekaru har 82 a duniya, amma hakan bai hana masa taka rawa sosai domin ci gaban al’ummarsa ba; Sarautar Ningi kamar kowace masarauta tana da mukamai daban-daban da ta baiwa mutane masu daraja da kima, kodayake muna kan harhada tarihin wasu da aka suke da rike da mukamai na sarauta a wannan masarautar, wadanda in hali ya bamu za mu buga nan gaba, sannan kuma za mu dubu wacce irin cancanta ne Sarki mai ci ya bi wajen yin nada-naden nasa, kuma za mu kalli masarautar Ningi tun daga tarihin lokacin da Sheikh Hamza ke gwagwarmaya zuwa yau mu gani shin yaya salon mulkin na da, da na yauzu, kasantuwar kun sani tarihi ya nuna Sarki Hamza ya yi yaki wajen yakar amsar haraji wanda a ganinsa hakan tamkar uzurawace ga jama’an da suke rayuwa a karkashin masarautun da ke amsar haraji mai tsanani.

Baya ga masarautar Ningi za kuma mu sake ninkayawa cikin tarihi domin sake nazarta tarihin wasu masarautun da suke Bauchi domin taskace tarihi don ‘yan baya, a dakwancemu wani jikon don dauko tarihin wata masarautar.

Wakilinmu na Bauchi Khalid Idris Doya ne ya yi Ninkaya cikin tarihi domin binciko mana tarihin Ningi.

07069724750 kidrisdoya200@gmail.com

 

Exit mobile version