Umar A Hunkuyi" />

NIS: Babandede Ya Gargadi Jami’ai 53 Da Aka Yi Wa Karin Girma

Babban Kwanturolan hukumar shigi da fici ta kasa, Muhammad Babandede, ya shawarci sabbin jami’an hukumar su 53 da aka yi wa karin girma da su guji duk wani nau’i na karban cin hanci da rashawa a kan aikin na su.

Babandede, wanda ya ba su wannan shawarar a lokacin da ake lika masu sabbin lambobin girman na su, wanda aka yi a Hedikwatar hukumar da ke Abuja, ya ce an yi masu karin girman ne a bisa cancantar su.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa hukumar ta yi wa jami’anta su 53 karin girma zuwa mukamin Kwanturola.

Ya kuma shawarce su da kar su yi amfani da khakin su na aiki da bindigoginsu a kan fararen hula, amma su kasance su masu kare su ne da tabbatar da tsaron lafiyarsu.

“A matsayinku na Kwanturololi, kun kai wani matsayi babba na mahukunta. Akwai bukatar ku san mene ne aikin ku, ku kuma zama jakadu nagari a wajen aikin na ku.”

“Za ku shugabanci mutane ne da suka fito daga rundunoni mabambanta, don haka ya zama tilas ku siffantu da ka’idojin wannan hukumar.

“Kamar yanda duk ku ka sani ne, Shugaba Buhari a koda-yaushe yana kira a gare mu da mu yi aikin mu da kyau, mu kuma nisanci cin hanci da karban rashawa, sannan mu rika girmama ‘yancin mutane.

“Tilas ku zama jajirtattu, kuma masu biyayya ga doka,” in ji Babandede.

Ya kuma yi kira ga sabbin manyan jami’an da su kasance masu nuna halin kirki da da’a a kan aikin na su.

Babban Kwanturolan ya ce masu, za a horas da su a kan dubarun shugabanci, da basirar aiki saboda su ne za su zama shugabannin hukumar a nan gaba.

Exit mobile version