Abdulrazaq Yahuza Jere" />

NIS Da NAPTIP Sun Sake Shan Damarar Yaki Da Safarar Dan Adam

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) da Hukumar Yaki da Fataucin Bil’adama (NAPTIP) sun sake shan damarar yaki da mummunar sana’ar nan ta safarar bil’adama zuwa kasashen ketare, lamarin da ke tilasta wa mata da kananan yara ‘Yan Nijeriya tsunduma cikin kangin aikatau da keta musu haddi da sauran na’u’o’in cin zarafi.

Da yake jawabi yayin gudanar da taro na hadin gwiwa a tsakanin hukumomin biyu a shalkwatar NIS da ke Abuja a yau Laraba, Shugaban NIS CGI Muhammad Babandede ya yi bayani game da muhimman sassan da hukumomin za su hada karfi da karfe wajen dakile hanyoyin da masu safarar bil’adama da sauran fasa-kwauri ke samun kudin shigar da suke aikata miyagun laifukansu; ta hanyar tabbatar da dorewar yaki da su.

Har ila yau, Babndede, ya ce gudunmawar da hukumomin za su bayar da sauran abokan kawance na kasashen duniya za su taimaka gaya wajen cimma nasara. Ya yi kiran a daina sake ta’azzara halin da wadanda wannan alkaba’i ya fada musu suka tsinci kansu a ciki, a matsayin wata hanya ta hukunci a kan ire-iren laifukan. Sai ya ba da shawarar cewa, ya kamata a daina gabatar da kananan yara a matsayin shaidu shari’o’in da ake yi a bainar jama’a domin riga-kafin jefa su cikin firgici. A maimakon haka a ba su kariya da kula da hakkinsu na ‘yan adam.

Sanarwar da ta fito daga jami’in yada labarun NIS DCI Sunday James, ta ruwaito shugabar NAPTIP, Imaan Ibrahim tana bai wa CGI Babandede tabbacin samun hadin kai da hadin gwiwar hukumarta wajen tabbatar da Nijeriya ta samu karin tagomashi da mutunci a idanun duniya ta fannin yaki da safarar bil’adama. Da kuma zama hukumar da ke kare martabatar matasan Nijeriya musamman mata da yara wadanda suka fi rashin samun gata.

Taron wanda aka shirya shi ta hoton bidiyo, ya gudana tare da dukkan manyan sassan NIS da NAPTIP da ke kula da iyakokin shige da ficen kasa da sauran sassan da ke aiki a cikin kasa.

 

 

Exit mobile version