Connect with us

LABARAI

NIS Da NCAA Na Shirin Bullo Da Hanya Guda Ta Tantance Mutane A Filayen Jirgi  

Published

on

Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS), da kuma Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama na Kasar nan (NCAA) suna duba yiwuwar bullo da wata hanya guda daya wacce dukkanin hukumomin da suka kamata za su rika bi wajen tantance masu shigowa kasar nan ta kan iyakokin manyan filayen Jirage saman kasar nan a lokaci guda ba tare da jeka-nan-shiga-can da ake yi ba a halin yanzun.

Hukumomin suna shirin daukar wannan mataki ne domin samun saukin wahalhalun da hakan ke janyo wa matafiyan.

Bayanin hakan yana kunshe ne cikin wata takardar sanarwa da Shugaban NIS, CGI Muhammad Babandede ya fitar ga manema labarai ta hannun Jami’in yada labarun hukumar ta shige da fice, DCI James Sunday.

Takardar ta ci gaba da bayanin cewa: “Hakan shi ya kawo bukatar samar da bayanan dukkanin fasinjojin da suke shigowa da masu barin kasar nan a kan lokaci a karkashin shirin nan na samar da bayanan fasinjoji (API), a dukkanin manyan filayen Jiragen sama na kasar nan domin kula da duk wata kai-komo na fasinjojin, wanda wannan babbar hanya ce ta samun bayanan fasinjojin tun kafin isowarsu cikin kasar nan domin samar da kyakkywan tsarin kula da tsaron kan iyakokin kasar nan kamar yanda dokar majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2396,ICAO ta kungiyoyin filayen Jiragen sama ta tanada, hakan kuma zai taimaka wa hukumomin gwamnatoci da ke filayen Jiragen saman da gwamnatocin kansu damar tattara bayanan fasinjojin ta hanyar da ta dace a manyan filayen Jiragen saman.

Shugaban hukumar shige da ficen ta kasa, Muhammad Babandede MFR, da babban daraktan hukumar kula da filayen Jiragen sama na kasar nan, Kyaftin Musa Nuhu, sun amince da su yi aikin hadin gwiwa a tare domin tabbatar da dukkanin hukumomin gwamnati da suke aiki a filayen Jiragen sama na kasar nan sun yi aiki a tare ta hanya guda a kan iyakokin kasar nan domin saukake wa fasinjoji hanyar da ake bi wajen tantance su ba tare da saba wa dokokin tsaron kasa a filayen Jiragen saman na kasar nan ba, ta hanyar yin amfani da na’urorin zamani tare da bin tsarin nan na tattara bayanai da kula da masu shigowa kasar nan, wanda shi ne mafificin tsarin da ake bi a sauran kasashen Duniya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: