Yusuf Shuaibu" />

NIS Ta Buɗe Sabuwar Cibiyar Amsar Bayanai Da Ƙorafe-ƙorafe

Cikin Sauƙi 'Yan Nijeriya Za Su Gabatar Da Ƙorafinsu - Babandede

Hukumar shige da fice ta ƙasa (NIS) ta sake buɗe sabon cibiyar amsar bayanan da ƙorafe-ƙorafi a nan gida Nijeriya da kuma ko’ina a faɗin duniya, bayan wadda ake da ita a baya ta yi gobara.
A ranar Laraba ce, hukumar ta buɗe sabuwar cibiyar domin ci gaba da karɓar saƙonnin abokan hulɗarta a ko ina cikin duniya.
A watannin da suka ka gabata ne ƙobara ta ƙone tsohuwar cibiyar ƙurmus, wanda hakan ya tilasta wa jami’an hukumar amsar bayanai da ƙorafe-ƙorafe a wayoyinsu na ƙashin kai, sai dai ba a ko ina ba, illa a hukumar. Wannan cibiya tana bai wa hukumar NIS damar amsaar bayanan da ƙorefe-ƙorafe a nan cikin gida Nijeriya da kuma ƙasashen ƙetare.
Da yake gabatar da jawabi b a wajen taron buɗe cibiyar, shugaban hukumar ta NIS, CGI Muhammad Babandede ya yaba wa babban jami’i da ke kula da wannan cibiya da kuma sauran jami’a da suke aiki tare, bisa yadda suke gudanar da aiki ba dare ba rana wajen ganin sun amsa bayanai da kuma warware ƙorafe-ƙorafen ‘yan Nijeriya a nan cikin gida da ma waɗanda suke ƙasashen waje.
Ya bayyana cewa gobara ta cinye tsohon cibiyar wanda aka tafka asarar kayayyaki na miliyoyin nairori, amma ba a yi asarar bayanai ko kaɗan ba. Ya ce wannan gobara ta zamar wa hukumar alkairi, domin a yanzu sun samu abubuwa da yawa wanda a baya ba su da shi.
“Gobara ta zamar wa hukumarmu alkairi, domin a yanzu mun samu dabarun aiki da kayayyakin wanda a baya ba mu iya mallaka ba.
“Mun samu damar ƙarin amsar bayanai da ƙorefe-ƙorafe dare da rana a wajen ‘yan Nijeriya na cikin gida da na waje. Wannan ba ƙaramin ci gaba muka samu ba.
“A kwanan nan ne hukumar da ke kula da ayyuka ta ƙasa ta yaba wa hukumarmu bisa irin yadda muke amsar bayanan tare da warware matsaloli da suke damun ‘yan Nijeriya a ɓangaren fasfo.
“Mun samu canje-canje a cikin wannan hukuma. ɗaya daga cikin wannan canjin dai shi ne, gudanar da ayyuka yadda ya kamata. Wanda a yanzu haka kai tsaye ‘yan Nijeriya za su iya biyan kuɗaɗen fasfo ɗinsu daga wayoyin hannunsu, wannan hakan zai rage cin hanci da rashawa a cikin hukumarmu. Ba sai ‘yan Nijeriya sun riƙe kuɗi ba zuwa hukumar NIS, za su biya kuɗi ne kai tsaye ta hanyar intanet, wanda wannan ba ƙaramin ci gaba ba ne a cikin hukuma ba,” in ji shi.
Haka kuma shugaban ya ƙara da cewa sun rage cinkoso wajen amsar bayanai da warware ƙorafe-ƙorafe wanda a yanzu cikin sauƙi ‘yan Nijeriya za su iya gabatar da ƙorafinsu sannan a magance musu nan take ba tare da ɗaukan wani lokaci ba.
Bugu da ƙari, Babandede ya bayyana cewa sun samar da kyakkyawan tsari na neman sabunta fasto daga wata uku zuwa wata shida, saboda ‘yan Nijeriya su sami isasshen lokacin sabunta fasfo ɗinsu. Ya ce ba nan kaɗai lamarin ya tsaya ba, sun samar da hanyoyin tunanar da ‘yan Nijeriya a lokacin da shekarun fasfo ɗinsu ya kusan ƙarewa, wanda hukumar za ta tura saƙon kar ta kwana a wayoyin mutane wajen tunatar da su kafin watanni shida fasfon ya daina aiki.
Wakazalika, manyan jami’ai da suka halarci bikin buɗe cibiyar wanda daga cikinsu akwai shugabar sashen kula da ingancin aiki, Misis Nnenna Akaijemel, da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Amos Okpu da shugabar kula da cibiyar amsaar bayanai da ƙorafe-ƙorafe, Obua CPP.

Exit mobile version