Jami’an Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) sun cafke wata bakuwar-haure ‘yar kasar Kamaru da aka yo jigilarta a motar fasinja, yayin da suke sintirin da suka saba na tsayar da ababen hawa domin bincike.
Sun cafke matar ce a wurin bincike na hadin gwiwa a kan iyakar kasa mai nisan kilomita takwas daga Ikom ta Kuros Riba, a kan titin iyakar kasa.
Jami’an, bisa jagorancin SI Umar Mala sun bankado matar ce mai suna Sally Kisob mai shekara 65, bayan sun fahimci ta silalo zuwa cikin kasa ne ta wurin shakatawar bakin teku na Efraya da ke Karamar Hukumar Etung na Jihar Kuros Riba.
Sanarwar da ta fito daga Jami’in hulda da jama’a na NIS, DCI Sunday James ta yi karin bayanin cewa an dauki bayanan bakuwar-hauren tare da mika ta ga jami’an hukumar na yankin iyakar kasa na Mfum domin bincike da kuma tasa keyarta zuwa kasarta ta asali.