Connect with us

LABARAI

NIS Ta Cafke Kwalekwale dauke Da Bakin Haure ‘Yan Kamaru Su 7

Published

on

Dakarun Hukumar Shige da Fice reshen Jihar Ribas da ke sintiri a gabar ruwa sun cafke wasu mutanen kasar Kamaru su bakwai a gabar ruwa ta Obong da ke karamar Hukumar Akpabuyo, yayin da suke kokarin kutsowa cikin kasar nan a wani jirgin kwalekwale.
An hana mutanen cimma burinsu na shigowa kasar tare da iza keyarsu zuwa kasarsu ta mashigin kasa na Ikang, kana aka kwace kwalekwalen da suka zo da shi.

Yayin da ake cafke kwale-kwalen baqin haure

Cafke mutanen su bakwai na daga cikin jerin kamen da ofisoshin NIS na jihohin Ribas da Akwa Ibom suka sha yi a baya a tsakanin iyakokin Nijeriya da Kamaru a karkashin umurnin da Gwamnatin Tarayya ta bayar na rufe iyakokin kasa.
Sanarwar da ta fito daga Jami’in yada labarun hukumar, DCI Sunday James ta bayyana cewa tuni dai Shugaban Hukumar Kula da Shige da Ficen ta kasa, CGI Muhammad Babandede MFR ya umurci ressan hukumar da ke kula da iyakokin kasa su rubunya sintirin da suke yi da tattara bayanai a gabobin ruwa da mashigin kasa na kan-tudu daban-daban domin hana bakin haure silalowa zuwa cikin kasar nan.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: