Daga Abdulrazak Yahuza Jere,
Jami’an Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) da ke aiki a Filin Jiragen Sama na Murtala Mohammed da ke Legas sun damke wasu ‘yan mata biyu yayin da suke kokarin shiga jirgin Kamfanin Jiragen Sama na Egypt zuwa Kairo, ta hanyar amfani da fasfuna biyu da aka yi shigar burtu da su.
An gano su ne bayan Na’urar Tantance Bayanan Fasinjoji (MIDAS) ta ki tantance fasfunan da suka zo da su saboda bad da kama da aka masu game da asalin masu fasfunan.
Bayan an titsiye su lokacin bincike, sun ce za su yi balaguro ne na kasuwanci ta hanyar wani wakilinsu da suka kira da “Muri” wanda aka yi ta kiran lambar wayarsa ba ya amsawa. Ana zargin shi ne ya samar musu da fasfunan na shigar burtu masu dauke da hoton namiji a bayansu kamar yadda Na’urar MIDAS ta nuna. Wannan abin da Muri ya yi babban laifi ne idan har ya tabbata shi ya yi wanda zai fuskanci hukunci a karkashin dokokin shige da fice na 2015.
CGI Babandede dai ya sake gargadi ga wadanda suke amfani da fasfon Nijeriya su daina yin sakaci miyagu suna fakar idanunsu su sace musu fasfo domin aikata miyagun laifuka wanda idan aka kama mutum da yi zai fuskanci hukuncin dauri a gidan yari ko cin tara.
‘Yan matan biyu dai na taimakon jami’an hukumar ta NIS da muhimman bayanai da za su taimaka a cafke Muri don hukunta shi, kamar yadda sanarwar da ta fito daga jami’in yada labarun NIS, DCI Sunday James ta bayyana.