NIS Ta Fara Bayar Da Ingantaccen Sabon Fasfo A Kano

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), ta sanar da fara bayar da sabon fasfo da aka inganta a babban ofishinta na fasfo da ke a Cibiyar Farm (Farm Centre) a birnin Kano.

An bai wa Gwamnan Kano Dafta Abdullahi Umar Ganduje da uwargidansa, Hajiya Hafsat Ganduje sabon fasfon, a yayin kaddamar da shi a Kano a hukumance a ranar 28 ga Oktoban 2019.

Da yake jawabi a wurin kaddamarwar, Gwamna Ganduje ya taya hukumar ta NIS murnar samun nasarar shigar da fasahohin kimiyya na zamani cikin ayyukanta, tare da bayyana cewa bullo da sabon fasfon da aka inganta ‘yar manuniya ce ga dukufar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi ta saukaka yanayin hada-hadar kasuwanci a kasar nan domin bunkasa kasar zuwa mataki na gaba.

A nashi bangaren, wakilin Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa, Muhammad Babandede, ACG TB Oyedeji, ya bayyana cewa babbar hikimar da ke cikin bullo d sabon fasfon ita ce inganta tsaron kasa da kuma saukaka yanayin hada-hadar kasuwanci, inda ya nunar da cewa sabon fasfon yana kunshe da alamomi na tsaro guda 25 ciki har da Lambar Katin Shaidar Dankasa (NIN).

Sanarwar da Jami’in Yada Labaran NIS, DCI Sunday James ya fitar ta nunar da cewa ofishin fasfo na Kano shi ne na biyu da aka fara bayar da sabon fasfon a wajen Babban Birnin Tarayya Abuja, inda aka tsara shirin ta yadda sannu a hankali sabon fasfon zai maye gurbin tsohon da ake amfani da shi.

 

 

Exit mobile version