Abdulrazaq Yahuza Jere">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home LABARAI

NIS Ta Gabatar Da Rahoton Ayyukanta Na Shekarar 2020

Rahoton Ya Nuna Kwazon Hukumar - Aregbesola

by Abdulrazaq Yahuza Jere
March 16, 2021
in LABARAI
1 min read
NIS Ta Gabatar Da Rahoton Ayyukanta Na Shekarar 2020

Wakilin ministan cikin gida Dakta Shuaibu Belgore (a tsakiya), CGI Muhammad Babandede (na biyu a dama), babban mataimakinsa DCG Isah Jere da sauran manyan jami'ai yayin kaddamar da rahoton

WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta gabatar da rahoton ayyukanta na shekarar 2020, a wani bangare na matakin da hukumar ta dauka a karkashin shugabancin CGI Muhammad Babandede na tattara rahoton ayyukanta a duk shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ne ya kaddamar da gabatar da rahoton a yau Talata 16 ga Maris na 2021 a shalkwatar hukumar da ke Abuja.

Ministan wanda babban sakataren ma’aikatar, Dakta Shuaibu Belgore ya wakilta, ya yi bayanin cewa rahoton ya nuna cewa NIS ta yi kwazo a shekarar 2020 wanda hakan ya fayyace irin dukufar da NIS ta yi a kan aiwatar da ayyukanta bisa jagorancin ma’aikatar cikin gida.

Hoton bangon farko na rahoton

Da yake yaba wa shugaban hukumar ta NIS, CGI Muhammad Babandede, wakilin ministan ya yi kira ga sauran hukumomin gwamnati su yi koyi da NIS wajen tattara bayanan ayyukansu a duk shekara.

A jawabinsa, CGI Babandede ya bayyana cewa duk da irin dimbin kalubalen da aka fuskanta a 2020 saboda cutar Korona, NIS ta yi tsayuwar daka domin ganin ba ta sare ba a kan ayyukanta da kuma ci gaba da gudanar da sauye-sauye masu ma’ana da ta tasa a gaba.

Babandede ya karfafa gwiwar ‘Yan Nijeriya su yi amfani da damar da aka samu ta gabatar da rahoton na shekara-shekara domin sanin aikace-aikacen hukumar, inda za a samu cikakken rahoton a shafin hukumar na intanet: www.immigration.gov.ng, kamar yadda sanarwar da hukumar ta fitar ta hannun jami’inta na hulda da jama’a DCI Sunday James ta nunar.
 

 

SendShareTweetShare
Previous Post

‘Yan Bindiga Sun Kona Makaranta Da Asibiti A Jihar Yobe

Next Post

‘Yan Ta’adda Sun Harbe Mutum 55 A Nijar

RelatedPosts

Ministan Tsaro, Bashir Magashi Ya Ziyarci Maiduguri

Ministan Tsaro, Bashir Magashi Ya Ziyarci Maiduguri

by Abdulrazaq Yahuza Jere
4 hours ago
0

Ministan Tsaro, Maj Gen Bashir Magashi (mai ritaya), a safiyar...

Azumi

Ramadan:  Nasarorin Da Ake Samu A Watan Azumi Na Da Tasiri Da Gudummowr Mata – In Ji Dakta Zainab Bagudu

by Abdulrazaq Yahuza Jere
13 hours ago
0

Daga:Umar Faruk Birnin-Kebbi Uwargidan Gwamnan Kebbi, Dakta Zainab Shinkafi Bagudu,...

Asibitoci

Muna Yaba Wa Gwamnatin Tarayya Bisa Inganta Asibitoci – Farfesa Jika

by Abdulrazaq Yahuza Jere
13 hours ago
0

Daga Mustapha Abdullahi, Shugaban da ke kula da babban asibitin...

Next Post
‘Yan Ta’adda Sun Harbe Mutum 55 A Nijar

'Yan Ta'adda Sun Harbe Mutum 55 A Nijar

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version