Connect with us

LABARAI

NIS Ta Gudanar Da Faretin Shugabanta Da Jawabi Ga Jami’ai Bisa Ka’idojin NCDC

Published

on

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), CGI Muhammad Babandede MFR ya bayar da umurnin cewa a gudanar da faretin karshen wata na shugaban hukumar tare da gudanar da jawabi ga jami’ai ta hanyar bin ka’idojin da Hukumar Yaki da Annobar Cututtuka ta NCDC ta shimfida da kuma amfani da shafin intanet wurin isar da sako.

Bisa wannan umurnin, shugaban hukumar da sauran manyan mahukuntanta sun bayyana a filin faretin ta hanyar bin ka’idojin da NCDC ta shimfida domin gabatar da jawabinsa na wata-wata ga daukacin manya da kananan jami’an NIS na fadin kasar nan, sai dai a bana abin ya bambanta ba kamar yadda aka saba ba, inda jami’an kan hallara a filin faretin, saboda ka’idar hana cunkoso da ba da tazara a tsakani ba tare da cudanya da juna ba.

Shugaban hukumar ya karanta umurnin da ya bayar na ayyuka daban-daban ga ressan hukumar na manyan shiyyoyi da ressan jihohi da sauran ressa na musamman da ke fadin kasar nan, kana aka aike da kwafen takardar umurnin ta shafin intanet ga daukacin wadannan rassan.

Sanarwar da ta fito daga Jami’in yada labarun NIS, DCI Sunday James ta yi bayanin cewa an kammala faretin shugaban hukumar na bana tare da aikewa da umurni ga dukkan ressan hukumar domin isarwa ga jami’an hukumar manya da kanana domin cike gibin da cutar Korona ta haifar da kuma ci gaba da gudanar da muhimman ayyukan da NIS ke gudanarwa a filayen jiragen sama da gabobin ruwa da iyakokin kasa na kan-tudu da sauran ofisoshin hukumar ciki har da shalkwatarta da ke Abuja.

Wakazalika, a yayin faretin da gabatar da jawabin shugaban hukumar na bana, CGI Babandede ya gode wa Kamfanin CCECC bisa tallafin kayan riga-kafin cutar korona da ya bai wa hukumar, inda ya ce abin ya zo a kan gaba. Sai daiya yi gargadin cewa NIS ba za ta taba lamuntar duk wani abu da zai karya dokar shige da ficen kasar nan ba, shi ya sa ma take yin duk abin da ya kamata domin tabbatar da cewa bakin da suka bi ka’idar doka ne kawai suke shigowa kasar nan ko zama a ciki ko kuma gudanar da halastaccen kasuwanci.

Ya kuma jaddada cewa lokacin da aka diba na afuwa ga baki su zo su yi rajista ya shude, don haka duk bakon-hauren da aka kama za a hukunta shi daidai da abin da doka ta gindaya.

Kayan riga-kafin Koronar da kamfanin ya tallafa wa hukumar da su wanda CGI Babandede tare da rakiyar wasu manyan mahukuntan NIS suka amsa, a yau Laraba 24 ga Yunin 2020, sun hada da kwalin takunkumin riga-kafi guda 9 masu kumshe da takunkumi 2000 kowane kwali, da kwalin rigunan kariya guda 11 masu dauke da riguna 50 kowane kwali da wata na’urar auna yanayin zafin jiki.

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: