NIS Ta Horas Da Masu Magana Da Yawunta Kan Yakar Bakin Haure

Daga Abdulrazaq Yahuza Jere

Mukaddashin Kwanturola Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), Isah Jere Idris, ya kaddamar da kashin farko na taron kara wa juna sani na kwana biyu ga jami’an hulda da jama’a da aka zabo daga sassa daban-daban na hukumar. Taron ya gudana ne a ranakun Laraba 24 da Alhamis 25 ga Nuwamba, 2021 a Otal din Watbridge, Uyo, Jihar Akwa Ibom.

An shirya horon na kwanaki biyu ne tare da hadin gwiwar wata kungiya mai zaman kanta ta kasar Sipaniya, FIIAPP mai taken: “Dabarun Sadarwa a Matsayin Ingantacciyar Hanyar Dakile Bakin Haure Da Fataucin Bil Adama”. Taron ya samu halartar Jami’an Hulda da Jama’a guda arba’in da uku (43) da aka zabo daga manyan shalkwatocin hukumar na jiha. Shahararrun mutane da suka hada da Jami’in Hulda da Jama’a na NIS, Mataimakin Kwanturola Amos OKPU na daga cikin wadanda suka gabatar da jawabai masu jan hankali ga mahalarta taron.

Da yake bude taron, Kwanturolan Hukumar ta NIS mai kula da Jihar Akwa Ibom, George Didel wanda ya wakilci mukaddashin Kwanturola Janar na Hukumar, Isah Jere Idris, ya bayyana taken taron a matsayin wanda ya dace musamman a yanzu da ake fama da matsalar safarar bakin haure da fataucin mutane. Ya yaba wa masu shirya taron, (FIIAPP) da suka dauki matakin bayar da gudumawarsu wajen bunkasa iya aiki ga jami’ai masu magana da yawun NIS wanda hakan zai kara gyara kimar hukumar.

Wakilin Mukaddashin Kwanturola Janar na NIS, Isah Idris Jere, George Didel yana jawabi a taron

Babban jami’in ayyukan FIIAPP a Nijeriya Mista Joseph Sanwo wanda ya wakilci shugaban kungiyar Mista Raefel Mois, ya ce taron bitar na ba da gudummawa ne wajen inganta ayyukan jami’an hulda da jama’a na NIS kuma kungiyar EU ce ta dauki nauyin gudanar da taron.

Muhimman batutuwan da taron horaswar ya kunsa sun hada da; cewa babban sauyin da ake samu na zamani a bangaren sadarwa ta ICT yana nuna buƙatar cewa dole ne masu aikin Hulɗa da Jama’a su saka hannun jari a cikin yunƙurin haɓaka aiki don ci gaba na zamani.

Haka nan ya kamata shuwagabannin Ma’aikatu da Ƙungiyoyi su ba Jami’an Hulda da Jama’a mahimmancin da suke da su don ba su damar yin aiki yadda ya kamata wajen kiyaye kima da martaba da kuma yaƙi da baƙin haure.

Jami’in hulda da jama na NIS, Amos Okpu yana jawabi a taron

Sannan ya kamata a samar da karin matakan inganta karfin jami’an hulda da jama’a a kai a kai don samar da manyan hanyoyin isar da sakonni a kan hijira ba bisa ka’ida ba.

Sanarwar da Jami’in hulda jama’a ACI Amos Okpu ya fitar ta kuma ce, taron ya nuna cewa ya kamata a ci gaba da aiwatar da wannan ƙoƙarin gadangadan don haɓaka kyakkyawar alaƙa tsakanin hukumar da abokan huldarta.

Taron na kwanaki biyu da FIIAPP, ta aiwatar, ya sami gagarumin tallafi daga Tarayyar Turai.

 

Exit mobile version