Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

NIS Ta Kaddamar Da Na’urar Tantance Baki A Filin Jiragen Sama Na Abuja

by
3 years ago
in LABARAI
5 min read
NIS Ta Kaddamar Da Na’urar Tantance Baki A Filin Jiragen Sama Na Abuja
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta yi nasarar sanya Nau’urar Tantance Bayanan Baki Masu Shiga Kasa (MIDAS), a babban filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a ranar Talatar nan.

Ita dai na’urar ta MIDAS an sanya mata kayan fasahar sadarwa ta zamani da ake aikin kula da iyakokin kasa da su, inda take karbar bayanan baki da tafiyar da su, da adanawa da tantance su a dukkan sassan iyakoki da aka shata, tare da bayar da sahihiyar kididdiga domin inganta tsaro da tsara manufofin aikin shige da fice da sauran tsare-tsare.

Na’urar wacce Ministan Cikin Gida Rauf Argebesola ya kaddamar, an samar da ita ce bisa hadin gwiwa a tsakanin Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) da Gwamnatin Danmak da kuma Hukumar Kula da Shige da Fice ta Duniya (IOM).

Labarai Masu Nasaba

’Yan Bindigar Da Suka Sace Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Nasarawa Sun Sako Shi

Wani Bene Ya Kuma Ruftawa Ya Danne Mutane A Legas

Da yake jawabi a yayin kaddamarwar, Ministan cikin gidan ya yi bayanin cewa na’urar tana da matukar muhimmanci ga tsaron Nijeriya musamman a kokarin da kasar ke yi na samun sahihan bayanai game dukkan bakin da ke shiga da ficewa daga cikin kasar.

Tun da farko da yake jawabi, Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa Muhammad Babandede MFR, ya bayyana cewa na’urar ta MIDAS wacce za ta yi aiki kan tsaron iyakar kasa, za ta kuma yi aikin duba bayanan shige da ficen mutanen da ba a yarda da su ba wadanda Hukumar ‘Yan Sandan Duniya ta ankarar a kansu. Inda ya nunar da cewa tuni aka sanya wannan na’urar a kan-iyakokin kasa na kan-tudu 14, sai kuma na ruwa guda biyu.

Ya kara da cewa bisa cigaban da aka samu zuwa yanzu, Hukumarsa ta kudiri aniyar sanya na’urar a wasu manyan filayen jiragen sama guda hudu da ke sassan kasar nan.

“Sanya na’urar tare da kaddamar da ita ta fara aiki, wani sabon tsari ne na kula da shige da fice a iyakokin kasa, kamar yadda yake kunshe a cikin kundin kula da kan-iyakokin kasa na NIS da za a yi aiki da shi daga 2019 zuwa 2023, wanda Ministan Cikin Gida Ogebni Rauf Aregbesola ya kaddamar a watan da ya gabata”, in ji Babandede.

Shugaban na NIS ya kara da cewa na’urar an kerata ce ta yadda za ta shigar da bayanan tafiye-tafiyen fasinjoji tare da daukar tambarin yatsunsu domin gano hakikaninsu, da tantance gaskiyar bayanansu, da duba sahihancin takardunsu na tafiye-tafiye, da tattara bayanan shige da ficensu a kan-iyakokin kasa da aka shata da sauransu.

Babandede ya kuma kara da cewa dukkan bayanan da na’urar ta tattara tare da adanawa mallakar kasar da take aiki da na’urar ce ita dai, amma tana ba da damar aika bayanan ga masu ruwa da tsaki na cikin kasa da wajenta.

Ya bayyana cewa sanya na’urar a kan-iyakokin kasa na kan-tudu da na ruwa ya taimaka gaya wajen inganta samun bayanan shige da ficen baki a kan-iyakoki.

“Yana da matukar kyau a fahimci cewa, galibin miyagu masu aikata manyan laifuka suna tafiye-tafiye ne ta jirgin sama, bisa sanya wannan na’urar ta MIDAS a manyan filayen jiragen sama guda uku na kasar nan, mun kimtsa tsaf wajen hana miyagu cin karensu babu babbaka a tsakanin kasa da kasa”, in ji Babandede.

Ya kuma lissafa sassan da aka sanya na’urar da suka hada da: kan-iyakokin kasa na kan-tudu guda uku da ke Jihar Kebbi, da na Sakkwato guda uku, da na Katsina guda uku, sai na Kuros Ribas guda daya da kuma na gabar ruwa guda biyu duk dai a jihar.

Sauran kan-iyakokin da aka sanya na’urar su ne na kan-tudu guda biyu a Jihar Jigawa, da guda daya a kan-iyaka na gabar ruwa Jihar Akwa Ibom, da na kan-tudu guda daya a Jihar Ogun, da guda daya a babban filin jiragen sama na Jihar Kano, da guda daya a filin jiragen sama na Legas sai kuma na Abuja.

Shugaban na NIS ya kuma bayyana cewa kwarya-kwaryar gyaran fuskan da NIS ta dukufa yi na inganta kula da shige da ficen kasa ta fara haifar da da mai ido, yana mai cewa, “ina mai farin cikin bayyana cewa mun samu cigaba a ayyukan da muke yi wajen tantance masu fita daga kasa da masu shigowa ciki a kan-iyakokin kasa da filayen jiragen sama. Ayyukanmu na tantancewa a manyan kan-iyakokin kasa na gabar ruwa da na kan-tudu sun inganta. Bisa amincewa da sabon fasalin aikin kula da iyakokin kasa ta nu’ura da gwamnati ta amince da shi, ba da jimawa ba dukkan kan-iyakokin kasarmu za su zama ana kula da su bai-daya,” in ji Babandede.

 

Wakazalika, shugaban hukumar ya ce sun samu nasarar fadada ayyukansu na bayar da izinin shiga kasa (biza) ta hanyar bullo da da tsarin bayarwa nan take lokacin da bako ya shigo cikin kasa ba domin bunkasa harkokin zuba jari na kai-tsaye daga waje ba kawai, har ma da tabbatar da cewa bakin da suka dace ne kawai ake bari su shigo kasa musamman ma bisa la’akari da yanayin kalubalen tsaron kasa da ake fuskanta yanzu haka.

Ya gode wa Gwamnatin Danmak kan tallafin da ta bayar na sanya na’urorin, yana mai cewa, “Muna godiya ga gwamnatin kasar ta Danmak musamman Jakadanta a Nijeriya wanda ya yi tsayuwar daka wajen tabbatar da an ba da kudin aikin da kuma kaddamarwa. Godiya ta musamman har ila yau ga mutanen Danmak da suka yo takakkiya tun daga kasarsu suka zo nan muka yi aiki da su cikin abokantaka. Ina mai tabbatar muku da cewa kudin harajin mutanen Danmak ba za su tafi a banza ba a karkashin wannan gwamnatin mai tarbiyya ta Shugaba Muhammadu Buhari, wadda a karkashinta hazikin minista irin Ogbeni Rauf Aregbesola ke sanya ido a kan Hukumar NIS.

“NIS ta karbi wannan aiki da hannu biyu-biyu a matsayin mallakinta bisa jagorancin Hukumar Kula da Shige da Fice ta Duniya (IOM). Mun yi aiki tare da ita ta bangarori daban-daban kuma mun samu nasarori a kai wajen zamanantar da ayyukan kula da shige da fice. Ina alfaharin bayyana cewa duka aikin sanya na’urorin MIDAS da na aikin rajistar baki ta intanet jami’anmu  na NIS ne ke yi. A karkashin aikin na’urar ta MIDAS an kafa cibiyar horaswa kan sarrafa na’urar a shalkwatar NIS. Cibiyar ta horas da Jami’an NIS sama da 300 a bangaren sanya na’urar MIDAS da sarrafa ta da kuma wasu 50 a wasu kwasa-kwasai na fasahar sadarwa ta zamani da suka jibanci amfani da na’urar,” in ji shi.

Babandede ya kuma gode wa Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama na Kasa ta FAAN bisa goyon bayan da ta bai wa NIS, wadda ya ce ba domin haka ba, da sanya na’urorin bai yiwu ba.

Har ila yau, ya yi godiya ga Ministan cikin gida bisa goyon bayan da yake bai wa Hukumar ta NIS, kana ya sake jaddada godiyarsu ga Gwamnatin Danmak da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Duniya (IOM), bisa amincewa su zo cikin Nijeriya su kera na’urorin na tantance baki masu shige da ficen kasa.

 

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Yawan Kayayyakin Da Aka Sayar A Ranar Gwagware Ya Nuna Yadda Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Kara Karfi

Next Post

Ahmad Musa, Ndidi Da Iwobi Sun Halarci Sansanin Super Eagles

Labarai Masu Nasaba

’Yan Bindigar Da Suka Sace Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Nasarawa Sun Sako Shi

’Yan Bindigar Da Suka Sace Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Nasarawa Sun Sako Shi

by Leadership Hausa
1 hour ago
0

...

Wani Bene Ya Kuma Ruftawa Ya Danne Mutane A Legas

Wani Bene Ya Kuma Ruftawa Ya Danne Mutane A Legas

by Leadership Hausa
2 hours ago
0

...

 ‘Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum 360 Da Sace 1,389 Cikin Watanni 3 A Kaduna

 ‘Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum 360 Da Sace 1,389 Cikin Watanni 3 A Kaduna

by Muhammad Bashir
3 hours ago
0

...

An Sace Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa Tare Da Kashe Dogarinsa

An Sace Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa Tare Da Kashe Dogarinsa

by Abubakar Abba
13 hours ago
0

...

Next Post
Muna Godiya Ga ‘Yan Nijeriya, Cewar Ahmad Musa

Ahmad Musa, Ndidi Da Iwobi Sun Halarci Sansanin Super Eagles

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

 

Loading Comments...
 

    %d bloggers like this: