Abdulrazaq Yahuza Jere" />

NIS Ta Kaddamar Da Sabuwar Shalkwatarta Ta Jihar Kaduna

Sabuwar shalkwatar NIS ta Jihar Kaduna da aka kaddamar a yau Juma'a

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta kaddamar da katafaren shalkwatar ofishinta na Jihar Kaduna, a wani bangare na kokarin da mahukuntan hukumar ke yi na kyautata muhallin aiki domin jami’ai su ji dadin gudanar da ayyukan da kasa ta dora musu.

Ministan cikin gida Ogbeni Rauf Aregbesola ya kaddamar da katafaren ofishin a ranar Juma’ar nan. Babban ofishin na NIS na Jihar Kaduna yana daya daga cikin katafaran ofisoshin hukumar na jihohi guda 13 da hukumar ta gina daga shekarar 2017 a karkashin shugabanta na yanzu, CGI Muhammad Babandede.

Da yake jawabi a yayin kaddamarwar, ministan, Ogbeni Rauf Aregbesola ya bayyana dukufar da gwamnatin tarayya ta yi wajen inganta wuraren ayyuka da samar da kyawawan muhallai ga jami’ai a fadin kasar nan domin su samu sukunin gudanar da ayyukansu bilhakki.

Sanarwar da ta fito daga jami’in hulda da jama’a na NIS, DCI Sunday James, ta bayyana cewa ministan ya yaba wa mahukuntan NIS bisa kudirin da suka tasa a gaba na gina dukkan manyan ofisoshin hukumar na jihohin kasar nan 36 har da Babban Birnin Tarayya Abuja.

Ministan Cikin Gida Ogbeni Rauf Aregbesola (a hagu),
Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru el-Rufa’i da Shugaban NIS Muhammad
Babandede yayin da suka ziyarci fadar gwamnatin jihar a yau Juma’a

A nashi bangaren, shugaban hukumar ta NIS CGI Muhammad Babandede ya ce samar da kyakkyawan muhalli na aiki shi ne muradi mafi kankanta da ake so masu daukar aiki kar su gaza cika wa ma’aikatansu, don haka ya nade kafar wandonsa ya dukufa wajen tabbatar da gina sabbin katafaran ofisoshin hukumar akalla guda biyu duk shekara tun daga 2017.

“Kaddamar da wannan katafaren ofishi ta sanya yau ta zama wata rana abar alfahari ga Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa musamman ga shugabanni da sauran jami’an da ke aiki a ofishin na Jihar Kaduna. Kamfanin Messrs Bonny Rose Investment and Supply ne ya gina shi a kan kudi N 208,130,821.35. A koyaushe mun sha jaddada cewa idan har muna so mu rika gudanar da ayyuka masu nagarta ga al’umma wajibi ne mu zuba jari mai tsoka wajen inganta ilimi da kwazon jami’ai da kuma kyautata muhallin da ake aiki.

“Hukumar a karkashin shugabancinmu ta aiwatar da ayyukan ababen kyautata jindadin ma’aikata a sassanta daban-daban na kasar nan daga 20016 zuwa 2020. Wannan sun hada da manyan katafaran ofisoshi na jihohi guda 13, gidajen kwanturololi 13, sansanonin jami’ai na bakin iyakokin kasa guda 12, da wasu sansanonin jami’ai guda 45 da kuma rukunin masaukai na jami’ai. Har ila yau. An samar da motocin sintiri da na kwanturololi da bas-bas da motocin daukar marasa lafiya, duk wadannan an yi ne domin kyautata jindadin jami’ai manya da kanana na hukumar. Yanzu haka kuma muna gina cibiyar fasahar sadarwa ta zamani wadda idan an kammala za ta bai wa hukumar damar tattara bayanai da adanawa bai-daya inda sauran hukumomi da ma’aikatu za su iya samun bayanan ‘yan kasa da bakin waje nan take.” In ji Babandede.

Ya kuma yi kira ga jami’an hukumar su saka irin wannan kokari da gwamnati take musu ta hanyar dukufa da aiki ka’in-da-na’in domin an ce “yaba kyauta tukwici”.

Wakazalika, a yayin da yake godiya ga Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru el-Rufa’i da Ministan cikin gida Ogbeni Rauf Aregbesola, CGI Babandede ya tabbatar da cewa jami’ansa za su cigaba da inganta ayyukansu tare da ba da gudunmawa gaya ga harkokin tsaro a jihar.

 

 

Exit mobile version