A kokarinta na tabbatar da tsaron iyakokin kasar nan, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta kaddamar da sansanin jami’anta na kan-iyaka a garin Ilase da ke Jihar Ogun wanda ya zama cikon na 15 a cikin jerin wadanda ta kaddamar a sassa daban-daban na kasar nan.
Shugaban NIS, CGI Muhammad Babandede ya kaddamar da sansanin a ranar Juma’a 22 ga Janairun 2021. Sansanin dai wani bangare ne na kwarya-kwaryar gyaran fuska da sauye-sauye da hukumar ta NIS take aiwatarwa a sashen kula da iyakokin kasa domin sauke nauyin da kasa da ta dora mata.
A jawabinsa yayin kaddamarwar, Babandede ya sake nanata kudirin shugabancinsa wajen tabbatar da cewa an samar da ire-iren wadannan sansanonin a dukkan iyakokin kasar nan domin karfafa sintiri na tsaro da kuma aiwatar da kyawawan manufofin da aka bullo da su na kula da iyakokin kasa kamar yadda ya kamata.
Ya bayyana cewa irin wannan sansanin zai kara kaimin yaki da bakin-haure wadanda ake fasa-kwaurinsu zuwa cikin kasa, da masu fataucin bil’adama da sauran miyagun laifukan da ake aikatawa a tsakanin iyakokin kasa da kasa.
Wakazalika, hukumar ta ce, kamar dai sauran sansanoni 14 da NIS ta riga ta kakkafa, shi ma sansanin na Ilase an kawata shi da kayan aiki na zamani da suka hada da na’urorin sadarwa da kayan more rayuwa domin jami’an hukumar su ji dadin sauke nauyin da aka dora musu na sintiri da sanya ido kan shige da ficen kasa a kan iyakoki.