A wani bangare na hadin gwiwar da suka yi domin tabbatar da kula da shige da ficen jama’a a iyakokin kasa a zamanance, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta karbi karin gudunmawar na’urar tantance bayanan jama’a masu shige da ficen kasa daga Gwanatin Kasar Kanada.
Na’urorin dai ana aiki da su ne wajen tantance irin mutanen da suke shiga ko fita daga kasa a kan iyakoki.
Da yake jawabi a yayin karbar na’urorin a Babban Filin Jiragen Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, ranar 4 ga Disambar 2020, shugaban NIS, CGI Muhammad Babandede, ya tabbatar da cewa ana fara amfani da na’urar; hukumar ta samu gagarumin ci gaba ta fuskar aikin tantance fasinjoji masu shiga ko fita daga kasa cikin kankanen lokaci.
Ya kara da cewa, zuwa yanzu, an sanya na’urorin a muhimman wurare daban-daban da suka hada da iyakokin kasa na filayen jiragen sama da na kan-tudu kuma wadannan sababbin da Gwamnatin Kanada ta bayar ta hannun Hukumar Kula da Shige da Fice ta Duniya (IOM) guda 63, za a yi amfani da su kamar yadda ya dace.
Sanarwar da jami’in hulda da jama’a na NIS, DCI Sunday James ya fitar a madadin shugaban hukumar, ta ce NIS ta rungumi amfani da na’urar ce domin bunkasa ayyukan kula da shige da ficen kasa tare da taimakon Kungiyar Tarayyar Turai da Kasar Japan da Jamus da Suwizilan da Danmak da kuma Nowai.
Sanarwar ta kara da cewa, a shekarar 2018 an kakkafa na’urar a manyan filayen jiragen saman kasar nan guda biyar da kuma wasu muhimman mashigan kasa.