Connect with us

RIGAR 'YANCI

NIS Ta Karbi ’Yan Nijeriya 13 Da Suka Dawo Gida Daga Togo

Published

on

Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa ta karbi ‘Yan Nijeriya su 13 da suka dawo gida daga kasar Togo.

Mutanen dai masana fasahar kere-kere ne da suka je Togo domin gudanar da aikin kakkafa na’urorin aikin masana’antu a can kasar.
Tuni dai NIS ta mika mutanen ga Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Jihar Legas domin yi musu gwaje-gwajen lafiya tare da kebe su kamar yadda Hukumar Shawo Kan Cututtukan Annoba ta kasa (NCDC) ta bayar da umurnin a yi wa dukkan wadanda za su shigo cikin kasa daga waje, domin dakile bazuwar cutar Korona.
A cikin sanarwar manema labarai da shugaban NIS, CGI Muhammad Babandede ya fitar ta hannun Jami’in yada labarun hukumar DCI Sunday James, an bayyana cewa Mashigin Seme-Krake babban mashigi ne na shiga cikin Nijeriya ko fita, inda ya yi iyaka da kasar Benin, don haka ya sa NIS ba ta sako-sako da sanya ido tare da gudanar da sintiri a yankinsa domin bankado masu bi ta barauniyar hanya.
Sanarwar ta kara da cewa namijin kokarin da hukumar ke yi na tabbatar da tsaron iyakokin kasa ya sa ana samun karin yawan mutanen da suke shigowa kasa ta Mashigin Seme-Krake tun daga lokacin da aka rufe iyakokin kasa.
Shugaban na NIS, CGI Muhammad Babandede ya shawarci ‘yan kasa maso dawowa gida su kauce wa bin barauniyar hanya ta cikin jeji domin kauce wa cafke su a matsayin masu laifi da kuma riga-kafin jefa kawunansu a cikin tarkon bata-gari da ke jefa rayukansu cikin mummunan hadari.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: