NIS Ta Sake Bude Shafin Fasfo Tare Da Gargadi Kan Hulda Da ‘Yan Bayan Fage

Daga Abdulrazak Yahuza Jere

Shugaban Hukumar Shige da Fice ta Kasa CGI Muhammad Babandede MFR, ya sanar da sake bude shafin aikace-aikacen Fasfo da kuma hanyar biyan kudi daga ranar 8 ga Yunin 2021 da misalin karfe 12 na dare don ba wa wadanda suka cancanci Fasfo damar nema da biyan kudi ga nau’o’in fasfon da suke bukata.

Shugaban ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Talatar nan ta hannun Jami’in hulda da jama’arta ACI Amos Okpu wacce aka aike wa LEADERSHIP A Yau.

An dai rufe shafin neman fasfon ne a ranar 17 ga watan Mayun 2021 biyo bayan umarnin da Ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya bayar domin baiwa jami’an hukumar damar biyan bashin fasfo da ya taru a duk cibiyoyin bayar da fasfo na hukumar.

Sanarwar ta yi bayanin cewa bisa sake bude shafin neman fasfon, sabon babin da aka bude na neman fasfo ya fara aiki wanda a karkashinsa za a rika gabatar da bukatar neman fasfo ta shafin intanet na hukumar mai adireshin www.immigration.gob.ng

Sannan ana sa ran masu neman fasfon su ziyarci shafin don gabatar da bukatunsu na fasfo da loda takardun da suka dace na fasfon don tantancewa da sarrafawa. Haka nan an samar da sashen da masu nema za su yi magana da jami’ai don su rika sa su a hanya da warware abin da ya shige masu duhu game da neman fasfon ko biyan kudi.

Hukumar ta ce bayan masu neman fasfo sun yi nasarar gabatar da bukatarsu kamar yadda ya kamata, za su iya zabar lokacin da suka ga ya kwanta masu don ganawa da su da daukar bayanansu kuma a duk inda suke ganin ya fi kwanta masu a rai a tsakanin cibiyoyin hukumar.

A karkashin sabon babin na fasfo, sabon wa’adin kammala aikin fasfo da bayarwa bayan mutum ya yi nasarar gabatar da bukatarsa shi ne mako shida ga sabbin masu neman fasfo, sannan wadanda suke da shi sabuntawa kawai za su yi, nasu zai zama mako uku a duk cibiyoyin da suka zaba.

Bugu da kari a sabon tsarin, ba a yarda kowa ya gabatar da bukatarsa ta fasfo ba in ba ta shafin intanet ba, haka nan an haramta biyan kudi hannu da hannu a kowace cibiyar fasfo.

Hukumar ta kuma ce duk wanda ya gabatar da bukatarsa ta fasfo za a tuntube shi ta adireshinsa na imel da lambar wayar da ya bayar yayin da yake gabatar da bukatar nema, da zarar an kammala fasfonsa. Bayan haka, hukumar ta NIS ta ware lambar waya ta musamman domin neman karin bayani a kan kowane irin kalubale da za a iya fuskanta wanda ita ce:08021819988.

Shugaban NIS, Muhammad Babandede MFR ya yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga ‘Yan Nijeriya musamman masu neman fasfo su guji yin hulda da mutanen bayan fage saboda an samar da tsari mai kyau da kowa zai bi cikin sauki domin samun biyan bukata.

Ya kuma gargadi jami’ai masu yin fasfo din da su guji aikata duk wata kumbiya-kumbiya da za ta kawo nakasu ga samun nasarar sabon tsarin na fasfo, yana mai cewa duk wanda aka kama da laifi zai dandana kudarsa.

Hukumar ta NIS dai ta samu nasarar biyan bashin fasfo da ya taru mata sama da guda dubu dari biyu da talatin (230,000) a tsakanin lokacin da bai wuce mako biyu ba kacal.

Wakazalika ta nada daya daga cikin manyan mataimakan shugabanta DCG Wunti a matsayin shugaban sashen kula da fasfo da sauran takardun tafiye-tafiye domin samun nasarar sabon babin da ta bude na fasfo.

A sabon babin dai an amince wa ‘Yan Nijeriya su fara neman sabunta fasfonsu tun ana sauran wata shida wanda yake hannunsu ya kammala aiki domin rage cunkosa da azalzala saboda bukatar gaggawa. Haka nan NIS ta bude sashen da mutum zai iya samun fasfo cikin sa’o’i 24 kacal bisa hadin gwiwa da bangare mai zaman kansa ta hanyar biyan karin wani kudi a kan kudin fasfon na ainihi kamar yadda ake yi a kasashen duniya da suka cigaba.

Exit mobile version