NIS Ta Sauke Nauyin Bashin Fasfo, Ta Kara Wa’adin Karba Da Mako Guda

Fasfo

 

Daga Abdulrazak Yahuza Jere,

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta bayyana cewa ta cika alkawarin da ta dauka na biyan bashin fasfon da ake bin ta wanda a dalilin hakan ta dakatar da karbar sabbin bukatun fasfo daga ranar 18 zuwa 31 ga watan Mayun nan da ya gabata.

 

Shugaban hukumar ta NIS (NIS), CGI Muhammad Babandede ya bayyana haka ga manema labaru a shalkwatar hukumar da ke Sauka, a hanyar filin jiragen sama na Abuja.

Babandede ya kara da cewa akwai wasu cibiyoyin aikin fasfo na hukumar kalilan da ba su kai ga karasa aikin da ke hannunsu ba kafin ranar 31 ga Mayun, amma akwai tabbacin za su kammala aikin a ranar 1 ga watan Yunin 2021.

A sakamakon wannan nasara da hukumar ta samu na sauke nauyin dimbin bashin fasfo da ke kanta, za ta bude fagen shigar da sabbin bukatun neman fasfo daga ‘Yan Nijeriya a ranar Larabar makon gobe wadda za ta kasance 9 ga Yunin 2021.

Sai dai kuma Muhammad Babandede ya ce har yanzu akwai fasfo sama da dubu arba’in da uku (43,000) da suka kammala aikinsu amma har yanzu masu su ba su zo sun karba ba. A cewarsa, wannan ta sa Ministan Cikin Gida Ogbeni Rauf Aregbesola ya amince a kara tsawaita wa’adin karbar fasfon da mako daya domin a bai wa ‘yan kasa damar zuwa su amsa.

Ya sake nanata kira ga duk wanda ya san yana bin hukumar bashin fasfo ya rika duba sakon wayarsa ta hannu saboda suna aika wa duk wanda aka kammala aikin fasfonsa sakon cewa ya zo ya karba. Ya nemi wadanda suka saka tsarin hana shigowar sakonni wayarsu su sauya hakan domin bai wa sakon da hukumar ke aikawa damar shiga wayoyinsu.

 

“A halin yanzu kowace cibiyarmu ta aikin fasfo tana da isassun takardun fasfo, kowa ya je amsa fasfonsa. Duk wadanda muka kammala aikin fasfonsu za mu sanya sunayensu a shafinmu na intanet bayan aikawa da sakon waya. Muna kara kira ga duk wadanda suka san sun shigar da bukatar fasfo a baya ba a yi masu ba, a yanzu an yi, su je su amsa. Muna bin tsari wajen bayar da fasfon saboda ka’idar rigakafin cutar korona, kamar yadda kwamitin shugaban kasa a kan yaki da korona ya bukata na hana cunkusuwar sama da mutum 50 a wuri guda, mukan raba masu karbar rukuni-rukunin mutum 50, idan wannan rukunin ya karba sai mu sake kiran wani rukunin. Haka muke yi tun daga karfe 6 na safiya har zuwa 6 na yamma.” In ji shi.

CGI Babandede ya ce ba karamar nasarar kammala wannan aikin hukumar ta yi ba, domin a lokacin da suka dakatar da yin sabbin fasfuna, suna da bashin fiye da guda dubu dari biyu (200,000) a kansu amma yanzu abin ya zama tarihi.

 

Har ila yau, shugaban na NIS, ya jaddada cewa wani ba zai iya karba wa wani fasfo ba, domin dole sai mai shi ya zo da kansa an gwada tambarin yatsunsa domin tabbatar da cewa nasa ne. Sai dai ya ce, “za mu iya yarda wani ya karba wa wani idan akwai kakkarfan uzuri kamar rashin lafiya. A nan sai mu sa wani amintaccen jami’inmu ya wakilce shi.”

 

Bugu da kari ya ce suna duba yiwuwar samar da wata fasaha da za su rika amfani da ita ta yadda idan za a sabunta wa wani fasfo ba dole sai ya zo ido na ganin ido ba. Yana mai cewa “za mu yi amfani da tsari mafi inganci wanda ba zai zama barazana ga sha’anin tsaro ba. Sannan da zarar mun bude shafin ci gaba da yin sabon fasfo za mu fara da wadanda suka fara gabatar da bukatarsu, sannan saura su biyo baya.”

Haka nan Babandede ya ba da tabbacin cewa wutar da aka cinna a ofishinsu na Abiya ba ta shafi fasfo ko guda daya ba.

 

Daga nan shugaban hukumar ya yi karin haske kan rasuwar daya daga cikin jami’ansu da aka kashe a can jihar ta Abiya, inda ya mika ta’aziyya ga iyalai da sauran abokan aikinsa.

 

Muhammad Babandede ya kuma ce ya gana da dukkan shugabannin manyan sassan hukumar dangane da matsalar da ke faruwa ta barazanar tsaro, inda ya nemi dukkan jami’an hukumar su kauce wa shiga rikicin kabilanci da kuma yin aiki kafada da kafada da sauran hukumomin tsaro musamman ‘yan sanda wajen kiyaye kayayyakin gwamnati da maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Duk dai a yayin jawabin nasa, ya sake gabatar da daya daga cikin manyan mataimakansa, DCG Wunti wanda zai karbi ragamar kula da dukkan ayyukan samar da fasfo da sauran takardun tafiye-tafiye da izinin shige da fice.

Idan za a iya tunawa dai, a lokacin da aka sanya dokar kulle saboda dakile cutar korona a Nijeriya a shekarar 2020, hukumar ta samu nasarar kammala aikin fasfo sama da dubu dari biyu da talatin (230,000).

Exit mobile version