Connect with us

LABARAI

NIS Ta Sha Damarar Shiga Shirin Wadata Kasa Da Abinci

Published

on

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa, CGI Muhammad Babandede MFR, ya yi alkawarin cewa hukumar za ta mayar da hankali sosai wajen tabbatar da cewa jami’anta manya da kanana sun tsunduma aikin gona gadan-gadan domin bunkasa wadata kasa da abinci ta hanyar kawance da Hukumar Bunkasa Noma ta Kasa (NALDA)

Dama dai hukumar ta nuna aniyarta ta yin kawance da NALDA ta fannin aikin gona, sa’ilin da Babban Sakataren Hukumar Yarima Paul Ikonne ya ziyarci shalkwatar NIS a ranar Alhamis da ta gabata.

Yarima Ikonne, ya karfafa gwiwar jami’an na NIS su dukufa ga aikin gona, kasancewar ita ce sana’a daya tilo da aka amince jami’ai masu sa kayan sarki su gudanar baya ga aikinsu na ainihi. A cewarsa, wannan ya yi daidai da kudirin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari mai taken “A Koma Gona”, wanda zai tabbatar da cewa hukumomi da kungiyoyi da daidaikun jama’a sun tsunduma aikin gona ka-in-da-na-in domin wadata kasar nan da abinci.

Shugaban NIS, CGI Muhammad Babandede ya yaba da bude kofar da NALDA ta yi a kan shirinta na sana’ar noma, inda ya yi alkawarin zai shigar da jami’an hukumarsa da ke sassan kasar nan cikin shirin domin haka ta cimma ruwa a muradin da ake son cimmawa na samun isasshen abinci a cikin kasa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: