Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa, CGI Muhammad Babandede ya sake nanata cewa wajibi ne duk wani mai neman sabon ingantaccen fasfo da hukumar ke bayarwa ya gabatar da lambar katin shaidar dan kasa.
A cewar Babandede, hakan ya zama tilas ne domin samun nasarar hade bayanan fasfo da na katin shaidar dan kasa wanda Hukumar NIMC ke bayarwa.
Sanarwar da ta fito daga hukumar ta NIS ta hannun Jami’in hulda da jama’a, DCI Sunday James, ta bayyana cewa bisa la’akari da wajibcin katin dan kasar wajen yin fasfo da kuma yajin aikin da ma’aikatan hukumar samar da shaidar dan kasar (NIMC) ke yi, Hukumar Shige da Fice tana fayyace cewa, an samar da cibiyoyin NIMC a wasu sassa na NIS ne saboda saukaka hada-hadar kasuwanci a kasa domin masu yin fasfo kurum ta yadda ba sai sun sha wahala ba wajen neman inda ake yin katin dan kasar ba.
Sannan bayar da katin shaidar dan kasa ba shi daga cikin hurumin NIS. Don haka duk kudaden da ake biya na samun katin dan kasa, ko na sauya bayanan katin ko wani kudi na daban da ya shafin katin ba shi da alaka da NIS, saboda haka hukumar ba ta ci nanin ba, nanin ba zai ci ta ba.
Bugu da kari, sanarwar ta umurci kai rahoton duk wani jami’in NIS da yake cajar kudi mara ka’ida a kan NIN ko fasfo ta hanyar kiran lambobin waya kamar haka: 07080607900; 0814199908; ko shafin intanet: nis.servicom@nig.immigration.org.ng.
NIS ta kuma ce shugabanta CGI Babandede ya kafa wata tawaga ta musamman da za ta rika sanya ido domin tabbatar da ana samun nasarar aiki a dukkan ofisoshinta.
“Don haka, ana kira ga dukkan masu neman fasfo su biya kudi ta shafin intanet domin kauce wa fadawa hannun bata-gari, sannan NIS tana kara jaddada wa al’umma kudirinta na cimma bukatunsu a kan kari,” in ji sanarwar.