Abdulrazaq Yahuza Jere" />

NIS Ta Yaye Jami’anta 456 Da Aka Daga Darajarsu Karo Na Biyu

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa, Muhammad Babandede MFR ya jagoranci manyan baki da sauran jama’a wajen shaida faretin yaye jami’an shige da fice da aka daga darajar zuwa manyan jami’ai, karo na biyu da aka gudanar a Makarantar Horas da Jami’an NIS da ke Kano.
Bikin yaye jami’an dai ya samu halartar shugabannin sojoji, sauran rundunonin jami’an tsaro da hukumomin kai dauki, da wakilan masarautu da bangarorin addini da kuma mazumuntan hukumar ta NIS da ke Birnin Kano.
Da yake gabatar da jawabi a wajen, Muhammad Babandede ya karfafa gwiwar jami’an da aka daga darajar tasu su nuna shauki kan sabbin mukaman nasu na sufiritanda, ta hanyar dukufa ka-in-da-na-in ga aiki da kuma kauce wa duk wani abu da ka iya zubar da kima da martabar hukumarsu ta NIS, tare da zama jakadun hukumar nagari a duk inda suke.
A yayin da yake bayyana cewa sahun wadanda aka yayen a wannan matsayin a jiya Asabar su ne suka fara cin gajiyar Sabon Kundin Horaswa na NIS da aka koyar da su da shi, Babandede ya kuma gargadesu game da zuwa kamun kafa a turasu aiki a wurare masu maiko.
Shi ma da yake jawabi, Babban Kwamandan Makarantar Horaswar ta NIS da ke Kano, CIS Isma’il Hamis, ya gode wa shugaban hukumar bisa goyon bayan da yake bai wa makarantar da kuma namijin kokarinsa kan tabbatar da jami’an NIS suna samun horo a-kai-a-kai.
Haka nan ya bukaci jami’an da aka yayen su saka karamcin da aka yi musu na horas da su wajen bunkasa aikin hukumar a duk inda aka turasu aiki. Ya kuma jinjina wa takwarorin Hukumar NIS bisa hadin gwiwar da suke yi na aiki cikin zumunci da mutunci tun daga lokacin da ya kama aiki a matsayin Kwamandan makarantar ta Kano
Sanarwar da Shugaban na NIS Muhammad Babandede ya fitar ga manema labarai ta hannun jami’in yada labarun hukumar, Sunday James, ta yi tsokaci kan bikin yaye jami’an na NIS da aka daga darajarsu karo na biyu, inda ta ce abin ya yi armashi kuma ya kayatar sosai.

Exit mobile version