Abdulrazaq Yahuza Jere" />

NIS Ta Yaye Mataimakan Kwanturola Janar Da Suka Halarci Kwas Na 10

Shugaban NIS CGI Muhammad Babandede

Babban Kwalejin Horas da Manyan Jami’an Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) da ke Sakkwato ta yaye masu mukaman kananan da manyan mataimakan Kwanturola Janar da suka halarci kwas na 10.

Shugaban Hukumar ta NIS, CGI Muhammad Babandede ya taya jami’an da aka yayen murna tare da yin kira a gare su, su yi aiki da abubuwan da suka koya da kuma kara wa hukumar cigaba, kasancewar ana sa ran ganin abubuwa da dama na kwazon aiki daga gare su a matsayinsu na shugabannin gudanarwa da ke tsakiya.

Babban Kwamandan Kwalejin ACG Isiyaku Yusuf ya gode wa shugaban hukumar Muhammad Babandede saboda goyon baya da gudunmwar da ya bayar da suka taimaka kwas din na 10 ya samu nasara, duk da cutar Kwarona ta kawo cikas ga abubuwa da dama.

Sanarwar da jami’in hulda da jama na NIS, DCI Sunday James ya fitar ta bayyana cewa an yi bikin yaye manyan jami’an ne ta hoton bidiyo wanda ya samu halartar shugabannin hukumomin tsaro da ke Sakkwato da Kwanturololin hukumar na jiha da kuma wasu kalilan daga cikin manyan shugabannin al’umma na Sakkwato.

Wakazalika mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Abubakar Sa’ad III ya albarkaci bikin yayewar.

 

 

Exit mobile version