Connect with us

LABARAI

NIS Ta Yi Bankwana Da Mataimakan Shugabanta Biyu Da Suka Yi Ritaya  

Published

on

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), CGI Muhammad Babandede MFR ya yi bankwana da wasu manyan jami’an hukumar guda biyu wadanda suka yi ritaya daga aiki.

Wadanda suka yi ritayar su ne: Babban Mataimakin Kwanturola Janar, DCG Nuruddeen Graham da Karamar Mataimakiyar Kwanturola Janar, ACG Tamprika Virginia Oyedeji.

A yayin gudanar da taron bankwana da su, CGI Babandede ya bayyana kewar da zai ji na yin aiki tare da su, kana ya bukaci sauran manyan jami’an da suke bakin aiki su kara jajircewa da sadaukar da kai domin ci gaba da aiki a matsayin tsintsiya madaurinki daya.

Sanarwar da ta fito daga Jami’in yada labarun NIS, DCI Sunday James, ta bayyana cewa shugaban hukumar ya jinjina wa daukacin manyan mataimakansa da ke biye da shi a matakin shugabanci da kuma kananan mataimakansa da ke madafun aiki daban-daban na hukumar wanda suka yi aiki tukuru a karkashin shugabancinsa wajen daga darajar NIS zuwa matakin da take kai a yanzu.

Ya shawarci dukkan manyan jami’an da suka halarci taron bankwanan su kara dukufa ga aikin ci gaban kasa da zai kara bunkasa hukumar ta NIS, a maimakon bijiro da wasu batutuwa da ka iya zama karfen kafa ga ci gaban hukumar.

Ya kuma yi godiya ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari (GCFR) wanda ya nada shi a matsayin shugaban NIS na 16 tare da bai wa hukumar damar cimma wasu daga cikin dimbin nasarorin da kasar nan ke tinkaho da su a yau.

Haka nan ya jinjina wa dukkan jami’an NIS bisa kokarinsu, kana ya yi kira gare su a kan cewa har yanzu ana bukatar kara jajircewarsu a aiki wajen kiyaye tsaron kasa ta hanyar kula da shige da fice da kuma mayar da kasar ta zama abar zabi ga masu zuba jari da hada-hadar kasuwanci ta hanyar inganta dukkan ayyukan da hukumar ke gudanarwa.

 
Advertisement

labarai