NIS Ta Yi Gagarumin Sauye-sauyen Wuraren Aiki Ga Manyan Jami’ai

Muƙaddashin Kwanturola Janar Isah Idris Jere Ya Nemi Su Ƙara Himma

Daga Abdulrazaq Yahuza Jere

A ƙoƙarinta na inganta ayyukan da suka rataya a wuyanta na kula da shige da ficen ƙasa da tsaron iyakoki, Hukumar Kula da Shige da Fice ta ƙasa bisa jagorancin muƙaddashin Kwanturola Janar, Isah Idris Jere ta yi sauye-sauyen wuraren aiki ga wasu manyan jami’ai.
Kamar yadda sanarwar da ta fito daga Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar ta NIS, ACI Amos Okpu ta bayyana, sauye-sauyen wuraren aikin sun shafi ƙananan mataimakan Kwanturola Janar (ACGs) da kuma Kwanturololi 26.
Takardar umarnin sauyin wuraren aikin wadda aka fitar a ranar 21 ga Janairun 2022, ta ce waɗanda aka yi wa sauyin zuwa sassan hukumar daban-daban sun haɗa da: Babban jami’in da ke kula da shiyya ta shida (F), ACG DE Amahian da aka mayar da shi zuwa Sashen Tsare-tsaren Bincike da ƙididdiga a shalkwatar hukumar, inda wanda yake sashen ƙididdigar ACG LE Oemi-Ockiya aka mayar da shi zuwa shiyyar Ibadan a matsayin sabon shugaba.
Haka nan an sauya wa Babban Jami’in Kula da Bincike da Bin ƙa’ida, ACG AO Esekhagbe wurin aiki zuwa Sashen Kula da Shige da Fice, yayin da ACG UA Auna da ya kasance Babban Jami’in Kula da Ofishin muƙaddashin Kwanturola Janar aka mayar da shi zuwa Sashen na Bincike da bin ƙa’ida.
Shi kuwa Babban Jami’in Kula da Aikace-aikace a shalkwatar hukumar, ACG OG Osisanya, an sauya masa wurin aiki ne zuwa Legas a matsayin sabon Babban Jami’in Shiyya ta ɗaya (A), yayin da ACG EI Inok da ke shugabantar Shiyya ta takwas (H) da ke Makurdi aka dawo da shi shalkwata a matsayin Babban Jami’in Kasafin Kuɗi.
Bugu da ƙari, sanarwar ta kawo wasu daga cikin Jami’ai masu muƙamin Kwanturola da aka yi musu sauye-sauyen kamar haka:
Kwanturola mai kula da Babban Ofishin Legas, AB Aliyu an dawo da shi shalkwata a matsayin Babban Jami’in Kula da Ofishin muƙaddashin Kwanturola Janar, yayin da Kwanturolar da ke kula da Kaduna kuma, Bagiwa Mani aka tura shi zuwa Babban Ofishin hukumar na Legas.
Kwanturolar da ke kula da Babban Ofishin Jihar Filato, K Nandap a yanzu an mayar da ita Filin Jiragen Saman Murtala Mohammed da ke Ikeja (Jihar Legas), inda Kwanturola Chris Nomhwaange kuma ya maye gurbinta a Babban Ofishin Filato.
Har ila yau, Kwanturola YU Gulma da ke Shiyya ta biyu (B) da Kwanturola NI Eneregbu na Sashen Ayyukan HRM, yanzu an mayar da su Iyakokin ƙasa na Seme da Mfun a matsayin shugabanni. Yayin da shi kuma Kwanturola ES Fagbamigbe aka mayar da shi Iyakar ƙasa ta Idi-Iroko, sai kuma Kwanturola G Bello da ke Babban Ofishin Jihar Kano da aka yi masa musanya da Kwanturola Muazu Abdulrazaƙ mai kula da Jihar Katsina.
Muƙaddashin Kwanturola Janar ɗin dai, Isah Idris Jere ya buƙaci manyan jami’an su zage damtse su ƙara himma wajen bayar da gudunmawa ga sauye-sauyen da ake yi na ci gaban hukumar.
Sanarwar dai ta ce sauyin wuraren aikin ya fara aiki ne nan take.

Exit mobile version