NIS Ta Yi Wa Hukumomin Gwamnati Fintikau A Fasahar Sadarwar Zamani –Babandede

Daga Abdulrazak Yahuza Jere,

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya (wato NIS), Muhammad Babandede ya jaddada cewa hukumar ta yi wa sauran ma’aikatu da hukumomin gwamnati fintikau a fagen amfani da fasahar sadarwa ta zamani.

Ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai na musamman da ya gabatar a shalkwatar hukumar a jiya Laraba.

Babandede wanda ya dauki lokaci mai tsawo yana bayani kan nasarorin da hukumar ta samu daga shekarar 2016 da ya karbi ragamarta, ya nunar da cewa an sauya akalar gudanar da ayyukan hukumar daga tsohon yayi zuwa na zamani ta hanyar amfani da na’urorin sadarwa na zamani da ke tattara bayanai da tantance su da kuma fitar da sakamako mai kyau a dan kankanen lokaci.

Domin shaida irin wannan ci gaba na amfani da fasahar sadarwa ta zamani a hukumar ta NIS, CGI Babandede da kansa ya zagaya da ‘yan jarida cibiyar fasahar domin gane wa idanunsu yadda ake tafiyar da aiki a zamanance.

Duk da cewa hukumar ta hana ‘yan jarida shiga da kayan aiki har da wayoyinsu na salula sassan da hukumar ke aiki da na’urorin na zamani saboda abin da ta kira da “tsaro”, kusan kowa ya nuna gamsuwa da abin da ya gani, a fuskarsa, kama daga bangaren tattara bayanai da tantance su har zuwa na sanya ido a kan iyakoki na kasa.

Shugaban hukumar ya bayyana cewa, cibiyar fasahar ta zamani ta zama matattarar bayanai da aiki da su ga duk hukumomin tsaron kasar nan, shi ya sa tuni hukumomin na tsaro daban-daban suka fara kawo ziyara domin hadin gwiwa da cin gajiyar cibiyar.

A cewarsa, sun gudanar da manyan tarurruka daban-daban na horaswa a kan shugabanci da tsara manufofin aiki da sake fasalta muhimman sassa na hukumar inda aka dunkule ayyukan fasfo da bayar da sauran takardun tafiye-tafiye a karkashin sashe guda.

Ya kara da cewa, a shekarar 2019 sun tsara kundi na musamman da hukumar take amfani da shi a matsayin jagora ga ayyukan kula da iyakokin kasa. Sai kuma sabon fasali da suka yi wa takardar izinin shiga kasa ta Biza wadda Shugaba Buhari ya kaddamar a farkon shekarar 2020. Kamar yadda ya ce, an yi wa Bizar tsarin matakai daban-daban domin ta taimaka wa habaka tattalin arzikin kasa da kuma share hawayen ‘Yan Nijeriya da ke da shaidar zama dan wata kasa baya ga Nijeriya, wadanda sukan fuskanci matsala yayin da suka yi shirin balaguro.

Haka nan ya tabo batun sabon fasfo da suka bullo da shi mai inganci da aka wajabta sanya lambar shaidar dan kasa a ciki don yaki da satar shaidar wani.

Bugu da kari, Babandede ya warware abubuwan da suka shige wa mutane duhu game da abin da ake nufi da fasfo da amfaninsa, inda ya kara da cewa a nan gaba, zamani zai zo da ba za a rika amfani da fasfo na littafi ba saboda ci gaban fasaha. Sannan ya ce hukumar tana nan ta dukufa wajen ganin ta warware matsalolin da cutar Korona ta jangwalo na rashin samun Biza da Fasfo. Kana ya yi albishir da cewa, kamar yadda hukumar ta raba ofisoshin fasfo a sassa daban-daban na kasar nan, za ta yi kokarin yin hakan a kasashen waje.

Domin saukaka wa mutanen da ke son zuwa gida Nijeriya amma wa’adin aikin fasfonsu ya kare, shugaban ya ce ga duk mai wannan lalurar zai iya shigar da bayanan fasfonsa ta shafin intanet na hukumar, inda zai samu amincewar dawowa gida daga ofishinsa, sai dai da zarar mai neman ya sauka gida, kai tsaye zai wuce ofishin hukumar da aka tsara domin sabunta masa fasfon.

Ya bukaci duk wani mai korafi game da wani abu da ya shafi hukumar, ya garzaya shafin intanet na hukumar kai-tsaye ya mika kokensa ta email ba sai ya yi hulda ga wasu ‘yan baya ga dangi ba.

Wakazalika, CGI Muhammad Babandede ya bayyana cewa daga yanzu wajibi ne ga duk wani dan kasar waje da ke aiki a kasar nan ana biyan sa ya rika biyan haraji. “Don haka ma, a yanzu sharadi ne ga duk wani dan kasar waje ya nuna shaidar biyan haraji yayin da ya zo neman sabunta takardar izinin zama a kasa.”

Ya kara da cewa, duk wani kamfani ko daidaikun jama’a da suka dauki wani dan kasar waje aiki, su tabbatar da yaba biyan haraji, idan ba haka ba, abin zai dawo kansu.

Har ila yau, Babandede ya yi gargadi ga ‘yan kasar waje da ke auren yaudara tare da ‘Yan Nijeriya domin kauce wa biyan haraji. Ya bayyana cewa akwai kamen da hukumar ta yi a kan irin hakan tare da nanata cewa za su ci gaba da zurfafa bincike domin bankado mayaudaran domin hukunta su. A cewarsa, ko da wani ko wata ‘yar kasar waje sun yi aure da ‘Yan Nijeriya, dole idan suna aiki ana biyan su, su rika biyan haraji.

A ci gaba da bayanin nasa, Babandede ya ce sun cafke wani dan kasar Sin da yake damfarar mutane a matsayin “jami’in” samar da Bizar Nijeriya.

Da ya juya kan kokarin da hukumar ke yi na kula da iyakokin kasa, Babandede ya ce sun kafa sansanin jami’ai guda 14 a sassa daban-daban da ke dab da iyakoki wadanda aka kawata da kayan kyautata jindadin jami’ai. Ya ce za su ci gaba da samar da sansanonin domin karfafa tsaron iyakoki.

Haka nan ya ce tun da ya karbi ragamar hukumar, a duk shekara sai an wallafa rahoton ayyukan da hukumar ta gudanar a shekara. Ba da jimawa ba ma aka kaddamar da na shekarar 2020 wanda ya ce yana nan a shafin intanet na hukumar domin al’umma su karanta.

Da yake amsa tambayoyin da ‘yan jarida suka yi masa a kan ko Nijeriya za ta shardanta riga-kafin Korona wajen ba da Biza, CGI Babandede ya ce ba zai goyi bayan hakan ba saboda an yi gaggawa idan aka dauki wannan matakin a yanzu saboda karancin allurar riga-kafin.

Ya buga misali da cewa, riga-kafin ana yi ne sau uku. Yayin da wani yake kan mataki na daya, shi wani ya tafi na biyu ko na uku, babu daidaito, don haka abin zai kawo rudani. A bari sai an samu nasarar yi wa mutanen duniya riga-kafin na Korona da kashi 50 a cikin 100 kafin a dauki irin wannan matakin.

Taron manema labaran dai ya samu halartar manyan mataimakan shugaban na NIS.

Exit mobile version