Connect with us

LABARAI

NIS Za Ta Ci Gaba Da Rajistar Bakin Waje Ranar 1 Ga Yuli

Published

on

A bisa yanda gwamnatin tarayya ta yi umurni da sassauta dokar hana zirga-zirga sannu a hankali a sassan kasar nan. Babban Kwanturolan hukumar shige da fice ta kasa, Muhammad Babandede MFR, ya umurci dukkanin Kwamandojin hukumar da su fara aikin yin rajistan bakin waje sannu a hankali, daga ranar Laraba, 1 ga watan Yuli, 2020.
Bayanin hakan yana kunshe ne cikin wata sanarwa da babban jami’in hulda da jama’a na hukumar, DCI James Sunday, ya fitar jiya Alhamis, 18 ga watan Yuni, 2020, a Abuja.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, a bisa aiki da wannan umurnin tilas ne a yi aiki da matakan kariya daga kamuwa da cutar korona kamar yanda cibiyar yaki da cutuka masu yaduwa ta kasa ta zayyana sau da kafa, da suka hada da:
Tabbatar da tsaftan muhallinn yin rajistan a kowane lokaci kafin a bari bakin wajen su shiga ciki.
Yin gwajin yanayin zafin jikin bakin wajen ta hanyar yin amfani da na’urorin gwajin zafin jikin da aka bayyana.
Samar da maganin kashe kwayoyin cuta da kuma sabulu domin wanke hannaye da aka tanadar a wuraren.
Tabbatar da yin amfani da takunkumin rufe baki da hanci (wanda tilas ne duk wanda bai sanya ba kar a bar shi ya shiga cikin wajen) a dukkanin cibiyoyin yin rajistan.
Lizimtar ka’idar nan ta nisantar juna a tsakanin wannan zuwa wancan da tazaran akalla mita biyu.
Samar da kofa guda daya rak ta shiga wajen yin rajistan domin kula da yawan masu shiga wajen.
Babban Kwanturolan hukumar ta shige da fice ta kasa yana sa ran dukkanin ma’aikata da masu neman yin rajistan za su yi aiki da wadannan ka’idojin sau da kafa domin kare kai daga yaduwar cutar ta korona daga wannan zuwa wancan da kuma kare rayukan al’umma.
Hukumar ta NIS dai ta samu nasarar yi wa bakin waje da ke cikin kasar nan dubu dari biyu da hamsin da biyar (255,000) rajista.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: