Connect with us

LABARAI

NIS Za Ta Gurfanar Da Indiyawa Biyu Da Suka Shigo Nijeriya Ta Barauniyar Hanya

Published

on

Mahukuntan Hukumar Shige da Fice ta kasa da ke kula da Filin Jiragen Sama na Murtala Mohammed da ke Legas, sun yi nasarar damke wasu Indiyawa biyu da suka shigo Nijeriya ba bisa ka’ida ba.

A jawabin da ya yi wa manema labaru, Kwanturolan NIS da ke kula da Filin Jiragen, CIS Abdullahi Usman, ya yi bayanin cewa an damke Indiyawan ne a lokacin da ake tantance Indiyawan da za a kwashe daga Nijeriya zuwa kasarsu, ta filin jiragen.
Usman ya kuma ayyana cewa, a yayin da ake daukar bayanansu, an gano cewa Indiyawan sun shigo Nijeriya ne ta iyakar kasa ta kan-tudu kuma suna da takardar shaidar amince musu su yi biza lokacin da suka shigo kasa amma suka ki gabatar da ita ga jami’an shige da fice a kan iyakar kasar.
Kwanturolan ya kara da cewa Indiyawan sun kasance a Kwatano na kasar Jamhuriyar Benin na tsawon wata guda, da yake suna da takardar izinin shiga kasar mai dauke da kwanan watan 9 ga Fabarairun 2020 sa’ilin da suka baro can suka silale suka shigo Nijeriya ta barauniyar hanya.
Sanarwar da Jami’in yada labarun NIS, DCI Sunday James ya fitar, ta tabbatar da cewa hukumar za ta gurfanar da Indiyawan su biyu, daya dan shekara 32, daya kuma dan shekara 29 da haihuwa domin hukunta su a karkashin dokar shige da fice ta Nijeriya domin su zama darasi ga saura.
A halin da ake ciki kuma, kimanin Indiyawa 446 ne aka kwashe daga Nijeriya zuwa kasarsu a ranar Asabar 20 ga watan Yunin 2020, a wani bangare na tsarin kwashe ‘yan kasashen waje daga kasar nan saboda annobar Korona.
Shugaban NIS, CGI Muhammad Babandede MFR ya gargadi bakin waje su guji karya dokar shige da ficen kasashen da suke yada zango ko zama a ciki domin kauce wa hukuncin da ka iya haramta musu shigowa Nijeriya ko kuma fuskantar hukunci mai tsanani daidai da girman laifukan da suka aikata.
Advertisement

labarai