Khalid Idris Doya" />

NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Bauchi Wa’adin Mako Daya Ta Biya Ma’aikata 10,000 Albashinsu

Kungiyar Kwadago ta Nijeriya reshen jihar Bauchi (NLC) ta yi zargin cewar, fiye da ma’aikata dubu goma na jihar Bauchi ba su samu albashin su na watan Yuli da ya gabata ba, tana zargin gwamnati da daukar wani salo na rage ma’aikata a jihar.

Kwamared Danjuma Saleh da ya ke yi wa ‘yan jarida bayani hakan ranar Litinin a garin Bauchi, ya bayyana cewar, lamarin ya shafi mafi yawancin ma’aikatun Gwamnatin jihar.

“Mun fahimci cewar fiye da ma’aikata dubu goma ba su samu albashi na watan Yuli da ya gabata ba. Mun fahimci hakan wani yunkuri ne Gwamnatin jiha na rage yawan ma’aikatanta,” in ji Shugaban kwadago na jihar, Kwamared Danjuma Saleh.

Ya ce ma’aikatun sun hada da ma’aikatar kula da muhalli, ma’aikatar al’adun gargajiya da yawon bude ido, ma’aikatan Majalisar Dokoki ta jihar, Hukumar kiwon lafiya tun daga tushe, Gidan Radiyon Bauchi, da dai sauransu.

Shugaban kwadago ya ce rashin samun albashin ya kuma shafi ma’aikata arba’in da biyu (42) na hukumar ilimi ta karamar hukumar (LGA) Toro da ma’aikatan kiwon lafiya saba’in da hudu (74) na karamar hukumar Bogoro.

Ya kuma yi zargin kwamishinan kananan hukumomin jihar da dagula lamuran dakatar da wasu ma’aikata da suka kunshi sakatarorin kananan hukumomi, da sakatarorin ilimi hadi da wasu ma’aikatan ba tare da bin matakan da suka dace ba.

NLC ta nemi gwamnatin jihar da gaggauta biyan kudaden kungiyoyi na alawus-alawus dinsu cikin hanzari ko kuma su dauki matakan da suka dace. Har-ila-yau, NLC ta zargi gwamnatin jihar da kin biyan kudin giratuti na tsoffin ma’aikata wanda shi ma ta nemi a gaggauta magance matsalar don gudun fushinsu.

Kan matsalolin da suke fuskanta, NLC ta baiwa gwamnatin jihar Bauchi wa’adin mako daya tak da shawo kan matsalolin albashi da alawus-alawus na ma’aikata ko kuma ta fuskaci turjiya daga garesu.

NLC ta yi batun cewa gwamnatin Bauchi ta dauko hayar wani kamfani mai suna Dynatech System Solutions tare da hannata masa batun biyan albashin, inda kungiyar ta ce ba ya ga dagula lamura babu abun da kamfanin ke yi, suna masu nuna rashin gamsuwarsu da kamfanin sakamakon rashin kwarewa.

Sai dai gwamnatin jihar Bauchi mai da martani da cewa wasu zarge-zargen duk rashin madafa ne, inda ta ce sam basu hana ma’aikata sama da dubu goma albashinsu ba.

Kwamishinan kudi na jihar Bauchi, Umaru Sanda Adamu, shine ya maida martanin a madadin gwamnati da cewa alawus na ma’aikatan lafiya da kungiyar ta yi korafi tunin aka shawo kan matsalar, yana mai cewa an samu haka ne sakamakon dan wani tangarda da suka fuskanta.

Kwamishinan ya ce zancen NLC na cewar ma’aikata dubu goma ba su samu albashinsu ba babu gaskiya a zancen, yana mai cewa mutum 350 ne kawai ba su samu albashinsu ba, ya kuma ce hakan ma ya faru ne sakamakon rashin gano cikakkun bayanai na ma’aikatan, a cewarshi suna nan suna ci gaba da aikin tantance ma’aikatan, a cewarshi duk ma’aikacin zahiri ba za su cinye masa albashinsa ba sam.

Kan zargi giratuti kuwa, ya shaida cewar gwamnatinsu tana ware wani kaso da take biyan bashin kudin giratuti tun lokacin da suka hau kan kujerar, don haka ne ya ce yanzu ma suna kan bakarsu na ci gaba da biyan kudin.

A cewar gwamnatin dukkanin matsalolin da suke akwai an samu haka ne sakamakon gyara da suke yi kan tsarin albashi da tantance ma’aikatan bogi, yana mai fadin cewa bata ganin ma’aikata ne ke janyo tangarda wa gwamnati kan batun albashi.

“A gaskiya duk abun da muke yi ba muna yi don mu cuci kowa bane, muna yi ne domin mu tantance ma’aikatan bogi da na zahiri da kuma tantance adadin albashin ma’aiktan jihar da ake biya domin mun gano akwai aringizo sosai.

Ya ce sun gano wasu na tafka almundahana da batun albashi don haka suka dukufa wajen tabbatar da gyara, a bisa haka ne ya ce suke toshe kofofin da suke gani na sata ne.

Kan zargin da NLC ta yi na cewar an kawo kamfani mai zaman kansa da ke kula da batun albashi wanda har kungiyar ta ce kamfanin ne ke dakula batun albashi, gwamnatin ta ce sam ba haka zancen ya ke ba, “Ma’aikata sune ke shigar da ma’aikatan bogi, su kuma wannan kamfanin ba ma’aikatan gwamnati bane don haka za su bi tsari wajen tsara yadda lamaru za su tafi daidai,” a cewar gwamnatin jihar.

Exit mobile version