Abubakar Abba" />

NNPC Ta Fara Gyaran Matatar Mai Ta Fatakwal

Matatun

Galveston, UNITED STATES: An oil refinery is pictured 22 September 2005 on Galveston Bay in Texas City, TX. Hurricane Rita threatens a large portion of the US oil and gas operations industry in the Gulf of Mexico and along the Texas coast just weeks after a devastating blow to the sector from Katrina. Oil producers and refiners were attempting to secure their facilities in the face of a storm that threatens about 27.5 percent of the industry, said Red Cavaney, president of the American Petroleum Institute. AFP PHOTO/Robert SULLIVAN (Photo credit should read ROBERT SULLIVAN/AFP/Getty Images)

Kamfanin NNPC ya sanar da cewar, ya fara gayaran matatar ta Fatakawal kashi na farko yadda za su dinga samar da danyen mai ganununa guda 210,000 a kullum.

Sanarwar  wadda aka fitar da ita a ranar Talatar  data gabata ta ce, matatar man ta Fatakwal har ila yau, zata samar da gangunan danyen mai 60,000 a kullum an kuma gina ta ne a shekarar 1965, inda a lokacin take samar da gangunan danyen mai 150,000 an kuma kaddamar da ita ne a shekarar 1989.

Babban Manajin Darakta na rukunonin kamfanin na NNPC Dakta Maikanti Baru ne ya kaddamar da fara aikin a matatar man ta Fatakwal a   bayan an shafe shekaru 19 ba sake yi mata wani gyra ba.

Bayanin na Dakta Maikanti Baru wanda Janaral Manaja na sashen hudda da jama’a NduUghamadu ya fitar a garin Abuja ya bayyana cewar, kamfanin Milan-based Maire Tecnimont S.p.A tare da hadin gwiwar kamafin cikin gida Tecnimont Nigeria aka bai wa kwangilar aikin.

A cewar NNPC, kamfanin Maire Tecnimont S.p  an sanya sunan sa a jiren kamfanonin a kasuwar musayar kudi  ta kasa.

Snarwar ta ci gaba da cewa, kamfanin Tecnimont Group yana gudanar da ayyukan sa a kasashe 40 da ke fadin duniya kuma yana da ma’aikanatan da yawan su ya kai kimanin 5,500.

Baru ya sanar da cewar, ana sa rana a zagayen aikin na farko, aikin na sarrafa danyen mai zai kai yawan kashi 60 bisa dari.

NNPC ya kara da cewa, ya janyo kamfanin Eni/NAOC  don ya dinga bayar da shawara akan gyaran matatar man ta Fatakwal.

A cewar sanarwar, aikin kashi na farko zai shafe watannin shida zai kuma hada da duba kayan aikin kuma a cikin karashen watan Maris na shekarar 2019 za’a fara gudanar da aikin.

Sanarwar ta kara da cewa, aikin kashi na biyu kuma kamafnin Engineering Procurement Construction tare da hadin gwiwar kamfanin JGC na kasar Japan ne za su aiwatar da shi.

Da yake yin jawabi a madadain sauran yan kwangilar, wani jami’ai mai suna Antonio Bella da ke aiki a kamafnin Eni ya ce, dukkan kamfanonin da zasu gudanar da aikin za su tura kayan aikin su zuwa matatar don tabbatar da an fara aikin a cikin nasara.

Suma da suke nasu jawabin a madadin kaungiyoyin ma’aiakata shugaban kungiyar PENGSSAN  Odor Ayiri, da kuma shugaban kungiyar NUPNNGW Dibiah Joseph sun yi alkawarin bai wa ma’aiktan goyon bayan da ya dace wajen gudanar da aikin.

In ba a manta ba kamafnin na NNPC tuni ya yi watsi da tsarin zuba kudi da yake yi a baya soboda yawan bukatar da ake gabatar masa ta kusan watanni sha biyu na tattaunawa.

Kamafnin na NNPC ya kasance ya koma yana biyan kudin kai tsaye, ya kuma kasance ya rarraba aikin zuwa kashi kashi tare da farawa akan matatar mai ta garin Fatakwal sannan kuma a wuce ga matatar mai ta garin Warri  data jihar Kaduna ta hanyar yin amfani dabaru iri daya.

Exit mobile version