Rahoton kamfanin mai na kasa (NNPC) ya nuna cewa, a cikin wata guda biyu a jeriya ya rasa samun riba a kasuwancinsa na sayar da mai, duk da karin farashi. Rahoton ya bayyana cewa, kamfanin ya sami karancin samun haraji a kasuwancinsa na sayar da mai a watan Yuli da watan Agusta duk da karin farashin mai.
Kamfanin mai shi yake da alkakkin rarraba mai ga ‘yan kasuwa da kuma tace mai. An samu raguwar a cikin kasuwancin sayar da mai a watan Afrilu sakamakon dokar hana zirga-zirga da gwamnati ta kafa domin hana yaduwar cutar Korona.
An samu faduwar sayar da mai na lita miliyan 941.22 a watan Afrilu daga lita biliya 1.65 na watan Maris, lita biliyan 1.73 na watan Fabrairu, sannan lita biliyan 1.19 ne a watan Junairu, kamar yadda rahoton NNPC ya bayyana.
Amma an samu farfadowa a kan sayar da mai a watan Yuni sakamakon janye dokar hana zirga-zirga wanda ya karu da lita miliyan 950.67, inda aka samu lita biliyan 1.34 a watan Mayu. An dai kara samun farfadowa na sayar da mai da lita biliyan 1.02 a cikin watan Ynuli, inda aka samu karin lita miliyan 946.47 a cikin watan Agusta.
A rahoton NNPC na water da ta ganata ya bayyana cewa, “gaba daya lita miliyan 950.66 na mai aka sayar ciki har da wanda aka rarraba wa ‘yan kasuwa a wata Agustan shekarar 2020, idan aka kwatanta da na watan Yulin shekarar 2020 an dai sayar da lita miliyan 1,036.16.
“Idan aka hada lita miliyan 946.47 na man fetur da lita miliyan 2.72 na gas da kuma litanmiliyan 1.47 na kalanzil, za a ga cewa an tafka asara a cikin watan.”
Ya bayyana cewa, an sami yawan kudaden da ya kai na naira biliyan 114.70 a cikin kasuwancin mai da aka sayar a watan Agusta, wanda ya gaza kai na naira biliyan 121.69 na watan Yuli.
Haraji daga bangaren mai ya ragu da naira biliyan 114.02 a watan Agusta daga naira biliyan 119.56 na watan Yuli, inda aka samu naira biliyan 133.23 a watan Yuni, kamar yadda kamfanin NNPC ya bayyana. Gwamnatin tarayya ta cire tallafin mai a watan Maris ta wannan shekara bayan rage kudin mai daga naira 125 zuwa naira 145 wanda ya ci gaba da haddasa karuwar farashin mai.
Hukumar yaddade farashin mai ta kasa (PPPRA) ta bayyana cewa, za a dunga yaddade farashin man ne bisa yadda kasuwa ta kama. Ta shawarci kamfanin NNPC da sauran ‘yan kasuwa da su dunga yayyade farashin mai a duk wata. hukumar PPPRA ta shirya cewa, za ta fitar da tsarin farashin mai na wata uku, amma ta gagara yin hakan a watan Agusta da watan Satumba, inda ta bar ‘yan kasuwa na kayyade farashin man tare da kara farashin man a wuraren sari. A ranar 8 ga watan Satumba, hukumar PPPRA ta bayyana cewa, ta cire hannunta daga kayyade farashin mai. Ta kara da cewa, kasuwa ce za ta dunga kayyade farashin man.
Farashin mai ya karu daga naira 158 zuwa naira 1662 a watan Satumba, inda ya karu a watan Nuwamba daga Naira 165 zuwa naira 170.