Yusuf Shuaibu" />

NNPC Ya Yi Bayanin Makasudin Cire Tallafin Mai

NNPC

Kamfanin main a Nijeriya ya bayyana dalilian da ya sa aka janye tallafin man fetu, wanda a sanar cewa lokacin bayar da tallafi ya kare. Shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari shi ya sanar da hakan a garin Abuja a  gidan talabiji. Kyari ya bayyana cewa, sakamakon faduwar farashin danyen a kasuwannin duniya, domin kudin man fetun za su dai-daita ba har sai an ga abin da kasuwa ta nuna. Ya bayyana cewa, duk da cewa kamfanin NNPC ba ta da alhakkin fitar da farashin kdanyen man fetur, kasar tana kokarin komawa a kan wani salo na siyar da fetur ne. Tana so ta ga yanayin bukata da samuwar man fetur su kasance madogara a farashin shi. A kwanan nan ne, gwamnatin tarayya ta rage farashin litar man fetur daga naira 145 zuwa naira 125. A ranar daya ga watan Afirilu, farashin litar man fetur din ya gangara zuwa naira 123.50 duk da kuwa daukacin ‘yan Nijeriya na tsammanin farashin ya gangara kasa da hakan.

Hukumar kula da farashin lalbarkatun kudin danyen man fetur ta yi bayanin cewa, faduwar farashin litar ya faru ne sakamakon faduwar farashin danyen man fetur a kasuwan duniya, saboda barkewar annobar cutar coronavirus. A lokacin da aka sanar da shi cewa, ‘yan Nijeriya na tsammanin raguwar farashin man fetur din fiye da haka. Kyari ya yi bayanin cewa, akwai dalilai masu tarin yawa da ke kawo ragowa a farashin.

Kyari ya ce, “na san mu na kokarin komawa tsari ne wanda yanayin bukata da samuwar man fetur din ne zai daid-aita farashin shi. A don haka ne na san cewa, kasuwa ce kadai za ta dai-daita farashin ta yadda kowa zai ji dadi.

“Faduwar farashin danyen man fetur a kasuwannin duniya zai bayyana ne har a kan sauran kayayyakin da ake samu daga danyen man fetur din ne da makonni hudu.

“Bana tsammanin gangar danyen man fetur za ta fadi kasa da dala 20 kamar yadda mu ka gani a makon da ya gabata. Ina da tabbacin cewa, farashin danyen man fetur zai koma yadda ya ke.”

Ya cigaba da cewa, kamfanin NNPC na fatan samar da danyen man fetur har ganga miliyan uku a  kan kowacce rana. Ya ce, daga jiya yanayin samar da man fetur dinmu ya karu har zuwa ganga miliyan 2.3.

Lamarin da ya shafe watanni ko kuma shekaru bai faru ba. Ya bayyana cewa, hakan suke fatan ya ci gaba da faruwa har a kai ga inda a ke so.

Exit mobile version