Ɗan majalisar jihar Kano mai wakiltar mazabar Sumaila, Hon. Zubairu Hamza Masu, ya bar jam’iyyar NNPP ya koma APC.
A cikin wasiƙar murabus da ya aika wa shugaban majalisar, Hon. Ismail Falgore, Masu ya bayyana cewa rikice-rikice da shari’o’in cikin NNPP a matsayin dalilin ficewarsa.
- Tsohon Dan Takarar Gwamna A NNPP A Jihar Ondo Ya Yi Murabus Daga Jam’iyyar
- 2027: PDP Ta Mutu, APC Na Shirin Sake Yin Nasara – Martanin Ganduje Ga Lamido
Shugaban majalisar ya karanta wasiƙar a zaman majalisa na ranar Litinin, inda ya bayyana cewa Masu ya fice daga NNPP tun daga ranar 12 ga Mayu, 2025, kuma ya samu amincewa ga shugabannin APC a dukkan matakan da suka dace su karɓe shi.
Ɗan majalisar ya kuma bayyana cewa wasu mutane daban-daban a matakin jiha da na ƙasa suna da’awar shugabancin NNPP, ciki har da Dr. Suleiman Hashim Dungurawa da Sanata Mas’ud El-Jibrin Doguwa a matakin jiha, yayin da Dr. Ahmed Ajuji da Dr. Agbo Major ke da’awar shugabancinta na ƙasa, tare da shari’o’in kotu da ke dagula jam’iyyar.