Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

NOA Ta Shirya Gangamin Wayar Da Kan Muhammanci Yi Wa Yara Rajistan Haihuwa

by Muhammad
February 20, 2021
in LABARAI
2 min read
NOA
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Muhammad Awwal Umar,

Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa (NOA) tayi hadin gwiwa da hukumar
kidaya ta kasa kan muhimmancin yi wa yara ‘yan kimanin shekara biyar rajistan haihuwa da hukumar kidaya ta kasa. Shirin wayar da kan a kananan hukumomi shida da suka hada da karamar hukumar Gbako A,Edati da Mashegu da Mariga da Bosso da Gurara gwaji ne kan muhimmancin
rajistan yara dan tabbatar da sun shiga cikin yawan jama’ar kasa.
Da yake bayani a taron manema labarai da hukumar NOA ta shiryawa
manema labarai, shugaban hukumar NOA ta jiha, Malam Yahaya Ibrahim
Gbongbo, yace sun shirya wannan gangamin wayar da kan ne a yankunan
karkaru sittin na kananan hukumomi shida a jihar a matsayin gwaji.
Ya ce, za su mayar da hankali wajen ganin shirin ya yi anfani a bangaren
ilimi koda zai kai ba za a dauki yaro makarantar boko ba sai da wannan
rajistan, siyasa da ilimin zamantakewa da zai iya bada damar ganin an
samu sahihin kididdigar ‘yan Nijeriya, a cewar sa a shekarar 2018 yara
arba’in da uku ne kawai aka yiwa rajistan da hukumar kididdiga a jihar
Neja.
Ya ce, rajistan haihuwa na samun koma baya duba da rikon sakainar kashi
da jama’a ke yi wa shirin wanda yana shafa tafiyar da harkokin gwamnati
ta hanyar karancin kudaden shiga, saboda haka jama’a na neman
ilmantarwa da sanin muhimmancin rajistan da hanyar da ya kamata su bi
wajen samun rajistan wanda tilas muka nemi hadin guiwa da hukumar
UNICEF ganin sun damu da bukatar ganin an samar da rayuwa mai inganci
ga yara masu tasowa, dan haka ina jin-jinawa hukumar UNICEF kan hadin
kan da ta bayar dan samun nasarar aikin.
Gangamin wanda zai fara talatar mako mai zuwa 23/02/21 zai dauki
adadin kwanaki biyar, wanda ake sa ran yiwa yara dubu arba’in rajista.
Hukumar ta ce za ta ware cibiyoyi hudu a kowace karamar hukuma dan
bai wa jama’a damar kawo ‘yayan su dan yin rajistan.
Da take amsa tambayoyin manema labarai, uwargidan gwamnan Neja, Dakta
Amina Abubakar Sani da ta samu wakilcin babbar sakatariyar ma’aikatar
jin dadin mata da walwala, Madam Kaltum Dauda Rufa’i, tace wannan
shirin abu ne mai kyau, kuma tunda yanzu za a fara ne da matakin wayar
da kai akwai yiwuwar jama’a za su taimakawa gwamnati wajen samun
kididdiga cikin sauki. Domin gwamnati na yunkurin tallafawa jama’a
amma rashin samun kididdiga na janyowa gwamnati hannun agogo baya,
domin duk wani kasafin gwamnati ya ta’allaka ne akan sanin yawan
adadin jama’a ta yadda duk abinda ta kawo kowa zai iya anfana.
Akwài yiwuwar nan gaba gwamnati tayi anfani da wannan damar wajen hana
daukar yara makarantun boko sai in suna da takardar shaidar haihuwa
daga hukumar kidaya kamar yadda yau gwamnati ke yunkurin hade lambar
NIN da asusun ajiya na na bankuna dan nuna muhimmancinsa.
Tsaro na da muhimmanci ga gwamnati, samar da wannan rajistan haihuwa
zai taimakawa gwamnati samun damar adadin yawan jama’a da irin matakan
da ya kamata kan tsaron rayuka da dukiyiyon su.

SendShareTweetShare
Previous Post

Jihar Nasarawa Ce Cibiyar Noma A Nijeriya  In Ji Minista Noma

Next Post

SHARHIN LITTAFI: Littafin Koyon Salatin Annabi Cikin Sauki

RelatedPosts

An Yi Wa Mukarraban Buhari Rigakafin Cutar Korona

An Yi Wa Mukarraban Buhari Rigakafin Cutar Korona

by Sulaiman Ibrahim
7 hours ago
0

  Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ayau...

Farashin Gangar Danyen Man Fetur Ya Kai Dalla 71.28

Farashin Gangar Danyen Man Fetur Ya Kai Dalla 71.28

by Sulaiman Ibrahim
7 hours ago
0

Daga Sulaiman Ibrahim A karon farko a 2021, farashin mai...

Naira

Naira Na Shirin Sake Faduwa Warwas – FMDQ

by Muhammad
14 hours ago
0

Za Ta Iya Kai Wa Dala 500 Cikin Mako Mai...

Next Post
Littafin

SHARHIN LITTAFI: Littafin Koyon Salatin Annabi Cikin Sauki

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version