Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Alh. Aminu Bello Masari ya bayyana cewa Noma da kiwo ne suka gina Nijeriya ba Man fetir ba saboda haka idan aka koma gona za samu arzikin da zai cigaba da rike wannan kasar ba tare da yin dogaro da Man fetir ba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da wata kungiyar wayar da kan manoma ta (Masari Agricutural Forum) ta kai masa ziyara a gidan gwamnatin jihar Katsina domin nuna goyan baya akan irin yadda gwamnatin jahar Katsina ta dauki harkar noma da mahimmanci.
Ya kuma kara da cewa, noman da ake yi yanzu noma wanda zai rika sarrafa amfanin gona ta yadda ‘yan Najeriya za su yi amfani da shi yadda ya kamata ba wai noma wanda za a kwashe abincin a kai wasu kasashe ba, wanda a cewarsa idan aka hanyar da ya kamata wajan yin noman to za a iya samarwa mutane fiye da kashin saba’in aikin yi a Najeriya.
Sannan ya kara bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari na daya daga cikin shuwagabanni masu karfin zuwa zuciya wanda ya tari aradu da ka, inda ya hana shigowa da abinci domin kawai muna mu samar da na mu abinci, saboda wadanda suke amfana da shigowa da abinci ba fa so suke ba, kuma yaki suke da abin, kai har yanzu suna karfi saboda suna da kudade a hannunsu.
“Shi noma inda ya sha banban da man fetir arzikinsa da kudinsa kai tsaye aljihun masu noma yake shiga, amma man fetir arzikinsa sayewa ake a biya gwamnati haraji amma noma da kiwo na talaka ne. Kuma Allah Ya ce duk mutumin da aka ba ruwa da kasa to an yi masa tarin arziki sai dai in mutun din ya ki” inji gwamna Masari.
Shi ma da yake nasa jawabin tun farko shugaban kungiyar wayar da kan jama’a akan harkokin kiwo da Noma na Masari Agricultural Forum Alh. Abdulrashid Ruma ya bayyana cewa kafa wanna kungiya ta so ya zo daidai da manufofin gwamnatin jahar Katsina na taimakon manoma.
Ya bayyana cewa suna shiga lungu da sako domin kara kai sakon gwamnatin jahar Katsina na baiwa Noma fifikon da ya kamata domin fita daga cikin halin rashin wadata nunawa matasa mahimmanci yin noma mai makon neman aikin gwamnati.
A cewar Abdulrashin Ruma noma shi ne kadai hanya mafi sauki na samarwa matasa aikin yi saboda haka ne ma suke kara jinjinawa shugaban kasa Muhammadu Buhari na kiran da ya yi na a koma gona.