Daga Umar Faruk, Birnin Kebbi
Mukaddashin shugaban kasar, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce ma’adinai da noma, zai kasance abin mayar da hankali ga Gwamnatin Tarayya don maido da tattalin arziki kasar Najeriya.
Osinbajo ya bayyan hakan ne a Argungu lokacin kaddamar da kanfanin shinkafar WACOT na Naira biliyan Goma( N10 biliyan WACOT Rice Mill ) a Argungu da ke Jihar Kebbi.
Ya ce za a ci gaba da zuba jari a aikin noma da ma’adanai da sauran wasu wurare domin samar da kamfanoni masu zaman kansu, da kuma wasu wuraren kasuwan ci, ya bayyana yunkuri na Gwamnatin Tarayya kan zuba jari a aikin noma da ma’adanai domin samun kudaden shiga ga kasa da kuma jahohin kasa nan don ciyar da harakokin kasar a matakin gaba.
Har ila yau Osinbajo ya yaba wa mutanen da ke zuba jari a cikin kanfanin shinkafa na WACOT domin shine zaya kawo ci gaba da bunkasa kanfunnan masu zamankan su a shirin bunkasa noman shinkafa da cashewa, musamman a kan ci gaban mutanen kasar Najeriya.
Ya yi kira ga masu zuba hannun jari su shiga cikin aikin noma, samar da aikin yi ga marasa aikin yimutanen, musamman idan akai la’akari kan rashin zuba hannun jari a masana’atu na Gwamnati da masu zaman kansu, rashin yin hakan ya haifar da asarar hanyoyin ayyuka a fagen noma da kuma ma’adanai dama sauran masana’atu na kasar nan.
Bagu da kari Mukaddashin Shugaban kasar ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya zata ci gaba da bada goyon baya ga kamfanoni masu zaman kansu “kasancewa cewa hanya ce ta ci gaba da kuma damar samun aiki yi ga jama’ar kasar Najeriya. ‘’
Hakazalika, ya nemi kanfanin WACOT da su fito da shirin horas da manoma dubu 5,000 domin kara samar da isashiyar shinkafa a kasar nan.
Shima a nashi Gwamna Atiku Bagudu ya bayyana cewa wannan gwamnatin ta karfafa karuwa shinkafa maiyawa da amfani a kasar nan daga ton biyu a kowace kadada zuwa ton 11 a kowace kadada.
Ya ce wannan hadin kai tsakanin jihar da kuma kamfanoni masu zaman kansu da baban banki Najeriya don bayar da gudummawar inganta samar da abinci da kuma abinci tsaro.
Har ila yau ya ce duk da haka, ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da bada goyon baya ga kananan da kuma manyan manoma domin karin noma da abinci a kasar nan.
Shima da ya ke gabatar da jawabin sa shugaban zartarwa na kanfanin WACOT Mill Nig. Ltd, Mr Rahul Sabara, ya ce kamfanin zai ci gaba da raya aikin horas da manoma dubu dari da ashirin( 120,000) a kowace shekara. Har ila yau ya ce zasu samar da aiki ga mutane dubu uku da dari biyar( 3,5000 ) a matsayin ma’aikatan kafanin na WACOT, yayin da manoma dubu hamsi (50,000) ne zasu ci gajiyar shirin tallafin noma na kanfanin nasu don samar da shinkafa ga kamfanin.
Har ila yau Ya ce kamfanin fara da daukar ma’aikata dubu daya kuma ‘yan asulin jihar kebbi kafin nan zuwa da wani lokaci. Hakazalika ya kara da cewa kanfanin zaya samar da shinkafa ton 400 a kullum jihar ta kebbi domin samun sauki ga ‘yan kasuwa.
Daga nan ya godewa mukaddashin shugaban kasa daGwamnatin jihar kebbi da kuma jama’ar jihar kan irin gudunmawa da goyun baya da aka ba kanfanin sa domin samun nasarar kaddamar da shi cikin nasara, batare da wata matsaba.