Connect with us

LABARAI

Noma: Majalisa Ta Nemi Gwamnatin Tarayya Da Ta Kammala Ginin Dam Din Kogi

Published

on

A ranar Talatan nan ne Majalisar Dattawa ta bukaci Ma’aikatan albarkatun ruwa da ta tabbatar ta hanzarta kammala aikin ginin Dam din Osara, da ke Jihar Kogi domin a bunkasa aikin Noma ta hanyar samar da ruwan noman rani da kuma wanda mutane za su sha.

Majalisar ta umurci kwamitin ta kan albarkatun ruwa da ya shiga tattaunawa da ma’aikatar albarkatun ruwan kan yadda za a kammala aikin ginin Dam din, wanda a cewar Majalisar Dam din shi ne babban wurin samun ruwa a Jihar, yayin da Dam din Ekuku ke biye masa.

Wannan kiran na Majalisar ya biyo bayan bukatar da Sanata Ahmad Salau Ogembe, ne ya gabatarwa Majalisar na neman gwamnati ta hanzarta aikin ginin Dam din.

Sanata Ogembe ya ce, gwamnatin tsohon Shugaba Babangida ce ta fara aikin ginin Dam din, a matsayin samar da wata hanya na wadata ruwan noman rani da kuma samar da ruwan sha.

Ya bayyana cewa, gina Dam din wata dubara ce na bunkasa kamfanin karafa na Itakpe da Ajaokuta, kasantuwan Dam din na Osara yana da kusanci kilomita 6 ne kacal tsakanin sa da kamfanin karafa na kasa, NIOMCO, da ke Itakpe, da ke kan hanyar Lokoja zuwa Okene.

Sanatan ya koka kan yadda aka nakasa aikin ginin Dam din da samar da dukkanin kayan aikin da ya kamata na ginin Dam din, wanda zai samar da ruwan noman rani da kuma tsaftataccen ruwan sha.

Ya kuma koka da yadda aka yi watsi da wannan mahimmin aikin da zai habaka tattalin arzikinmu ba kawai ga al’umman Jihar Kogi kadai ba, da ma al’umman kasa bakidaya.

Sanata Ogembe ya yi gargadin, “Kasancewar Jihar Kogi ce kofar da ke tsakanin Kudu da Arewacin kasarnan, ba za a iya tantance rashin barkewar annoba ba sabili da rashin tsaftataccen ruwan sha.”

“A taswirar kasarnan Kogi ce a tsakiyar Nijeriya. Allah Ya albarkaci Jihar da albarkatun ruwa, a matsayin ta na mahadar manyan tafkunan nan biyu, Kogin Neja da Kogin Benuwe.

Da yake goyon bayan wannan kudurin, Shugaban masu rinjayen Majalisan, Sanata Ahmad Lawan, ya yi nu ni da cewa, matukar aka kammala aikin ginin Dam din, zai samar da karin ayyukan yi, da kuma arziki ga al’ummar na Jihar Kogi da ma kasa bakidaya.

Sanata Lawan, ya karfafa mahimmancin Dam din ga kokarin gwamnatin tarayya na habaka ayyukan noma ba ma kawai domin wadata al’umma da abinci ba har ma yadda za a inganta rayuwar ‘yan kasan.

Ya kuma yi nu ni da yadda wannan gwamnatin ta iya rage yawan shinkafar da ake shigowa da ita kasarnan a cikin shekaru uku kacal da ta yi da kashi 90, ya na mai imani da cewa, akwai yiwuwar a ma daina shigowa da shinkafar kwata-kwata ya zuwa shekara mai zuwa, lokacin da mu kanmu za mu fara fitar da shinkafar da ma wasu kayan zuwa kasuwannin duniya na waje.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: