Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Dakta Nasiru Yusif Gawuna ya jaddada bukatar da ake da ita na samun cikakken hadin kai tsakanin masu ruwa da tsaki a harkar noman Alkama a fadin kananan. Kamar yadda Daraktan yada labaran Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Hassan Musa Fagge ya shaidawa LEADERSHIP A YAU.
“Akwai bukatar masu ruwa da tsaki su fahimci juna domin habaka noman Alkama kamar yadda manoman shinkafa keyi a kasarnan, domin inganta cigaban noman Alkama,” inji shi.
Mataimakin Gwamnan ya bayyana Haka ne a ranar litinin a Kano Lokacin bikin ranar manoman Alkama da kungiyar masu sarrafa Fulawa suka shirya a karamar Hukumar danbatta dake Jihar Kano.
Ya ce, zabar inganta noman Alkama da Jihar Kano tayi abune da aka tsara, idan akayi la’akari da muhimmacin gudunmawar da Alkama ke bayarwa ga shirin samar da abinci a cikin gida, fitar dashi waje da kuma Inganta harkar noman kamar yadda ake bukata.
Ya kuma bayyana cewa Gwamnatin Jihar Kano karkashin Jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje zata ci gaba da hada hannu da masu sha’awar cigaban harkar, musamman manoma da kuma sauran al’umma da kungiyoyin dake cikin kasarnan wajen samar da kyakkyawan yanayin da zai taimakawa inganta noman Alkama acikin gida ta hanyar inganta samar da kayan aikin noma, sarrafa alkamar da cinikin fulawa.
Daga nan sai ya jinjinawa kokarin Gwamnati tarayya bisa goyon bayan da take baiwa harkar noman, haka kuma ya yabawa kungiyar masu samar da fulawa ta kasa bisa shigar da manoma ta hanyar aiwatar da ingantattun tsare tsaren samar da bashin noma a kananan Hukumomin danbatta, Garun Malam, Bunkure, Kura da Ajingi.
Da yake gabatar da jawabinsa Ministan Ma’aikatar Noma da Raya Karkara, Alhaji Sabo Nanono ya bukaci manoman alkamar su kara himmatuwa, musamman ganin yadda kowace shekara Gwamnati tarayya ke samu gibi ta hanyar shigo da kayan amfani daga kasashen waje.
“A cikin shekaru hudu da suka gabata, an shigo da alkamar sama da Naira Tiriliyon 2.2 cikin kasarnan, amma zuwa yanzu akwai muhimman tsare tsare da aka bujiro dasu domin habaka noman Alkama don rage shigo da ita daga waje.
“Akwai bukatar samar da wadataccen iri da kuma kirkirar kananan masana’antu ta hanyar zuba jari a harkar noman Alkama domin rage shigo da ita daga kasashen waje inji Nanono.”
Da yake jawabi tunda farko shugaban kungiya manoman Alkama na kasa, Alhaji Salim Muhammad ya bayyana cewa, wannan taro ya nuna a bayyane amfani da Ingantaccen tsarin noman Alkama na kara habaka kwarai da gaske a kasar.
Daga nan sai ya bukaci Gwamnatin Tarayya da Jihohi dasu ci gaba da taimakawa sashin noman Alkama da kayan noma irin na zamani.
Taron ya samu halartar shugaban kwamitin harkokin noma na Majalisa wakilai ta tarayya Manniru Babban dan’agundi, shugaban kungiyar sarrafa Fulawa na kasa, shugaban shirin noman Alkama na Sarah Huber na Nijeriya Alhaji Faruk Rabi’u Mudi.