Sama da manoma dubu 94 da mafi yawancinsu matasa ne su ka amfana da shirin Gwamnatin Tarayya na Anchor Borrowers a bangaren noman auduga a jihohin Kano da Jigawa.
Sanarwar hakan tana kunshe ne a cikin takarda da mai magana da yawun manoman da suka amfana da shirin, Yusuf Alhaji, inda ya ce sun ci gajiyar ce sakamakon kokarin Mataimakin Shugaban kungiyar Manoman Auduga ta kasa NACOTAN, Alhaji Munzali Dayyabu Taura, saboda kaddamar da bikin tantancewa na karfafa wa matasa shiga harkar noma na auduga.
Ya ce, a cikin mutum dubu 151 a jihohi 27 da ke cikin shirin Anchor Borrowers, jihohin Kano da Jigawa, su na da mutum dubu 94 da su ka ci gajiyar shirin, saboda kwazo da jajircewar Alhaji Munzali Taura.
A cewar wadanda suka amafana, burin Mataimakin Shugaban kungiyar ta kasa ta shi ne ya shigar da matasa su rungumi harkar noman auduga, sannan a talalfa wa kamar mutum dubu 100 a jihohin Kano da Jigawa.
Wadanda suka amfanar sun kuma yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya cigaba da bai wa harkar noma kulawa, saboda muhimmancinta ga al’ummar Arewa a bangaren tattalin arziki da yadda take samar da ayyukan yi kai-tsaye.